✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar tukunyar gas ta jikkata mutum 20 a Kano

Shaguna da dama sun kone, an garzaya da mutanen da wutar ta kama asibiti

Akalla mutum 20 sun jikkata a sanadiyyar fashewar tukunyar iskar gas a unguwar Sheka da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

Wani mazaunin unguwar, Malam Idi ya ce shaguna da dama sun kone a sakamakon tashin wutar bayan tukunyar gas din ta yi bindiga a wani shagon sayar da gas din girki.

“Mutum 20 ne lamarin ya ritsa da su, kuma an garzaya da su zuwa asibiti,” a cewar kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif.

Malam Idi ya ce yawanci mutanen da wutar ta kama suna shagon sayar da gas din girkin ne, da kuma masu shagunan da ke kusa da wurin.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ya  ce lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da dare, a dalilin wani mutum da ke suyan kifi a kusa da shagon gas din.

“Mun samu kiran neman agaji da misalin 7:04 na dare daga wani mai suna Adamu Muhd cewa gobara ta tashi a unguwar Sheka Karshen Kwalta, Karamar Hukumar Kumbotso.
“Da zuwanmu sai muka iske wani gini yana ci da wuta; a sanadiyyar wani mai suyan kifi da ke kusa sa shagon sayar da iskar gas,” inji shi.