Akalla yara biyar sun mutu bayan wani Gurneti da suke wasa da shi ya tarawatse a garin Ngala na Jihar Borno.
Lamarin dai ya faru ne ranar Alhamis a garin da ke dab da kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru, kamar yadda wani dan sa-kai a yankin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.
- Buhari ya dawo daga Landan bayan kwana 18
- Dan Arewa ne kadai zai iya lashe wa PDP zabe a 2023 – Dokpesi
“Yaran su biyar sun dauko Gurnetin ne lokacin da suke kiwo a wajen garin, inda ya fashe a hannunsu, lokacin da suke wasa da shi,” inji Umar Kachalla, wani dan sa-kai a yankin.
“Biyu daga cikinsu sun mutu ne nan take, ragowar ukun kuma sun mutu a asibitin Mada, da ke kasar Kamaru.” inji shi.
Kazalika, shi ma wani dan aikin sa-kan, Umar Ari ya bayar da makamancin wannan bayanin inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis.
Ari ya ce har yanzu burbushin Gurneti na ci gaba da yin barna a yankin, musamman a kan yara kanana wadanda ko dai suke mutuwa ko kuma su jikkata.
A watan Agustan 2014, mayakan kungiyar Boko Haram sun taba kwace iko da garin na Ngala da na Gamboru da ke da makwabtaka da shi.
Sai dai a shekarar 2015, sojojin Najeriya da gudunmawar na Chadi sun kwato garuruwan Bayan kwashe watanni suna kai hare-hare.
Ko a watan Disamban 2019, mutum tara sun mutu, 26 kuma sun jikkata lokacin da wani abin fashewa ya tashi a wata gada mai cike da cunkoso da ta hada garuruwan Gamboru da Fotokol.
Mazauna yankunan dai sun yi zargin cewa ’yan ta’addan Boko Haram ne suke ba yaran kyautar Gurnetin a matsayin kayan wasa. (AFP)