Mazauna garin Ilorin sun shiga cikin firgici sakamakon fashewar iskar gas da ya girgiza garin
Gas din ta yi bindiga ne wani gidan mai da ke kusa da Tashar Motar Offa da ke garin, lamarin da ya sa mazauna guje-gujen neman tsira, har wasunsu suka samu rauni.
- ’Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Sarkin Birnin Gwari
- Riz Ahmed: Musulmin farko a karbar kyautar Babban Jarumin Hollywood
- An shiga rudani a Kaduna kan umarnin bude makarantu
Masu baburan haya da masu sayar da kaya da sauran jama’a sun yi ta kafa me na ci ban ba ki ba, bayan fashewar iskar gas din a wani sanannen gidan mai.
Wata ganau kuma mai shago a kusa da gidan man ta ce, “Kawai sai muka ji wata kara da hayaki ya mamaye gidan man, sai muka fara gudun neman tsira ba tare da sanin abin da ke faruwa ba.
“Mutane da dama sun samu raunuka, musamman wasu da ke cikin gidan man kamar ‘yan talla, masu ba da mai da masu saya ma sun ji rauni”.
Shi ma wani shaida ya ce “Fashewar ta faru ne da safiyar Laraba, a lokacin da ake sayar da gas, amma nan da nan aka shawo kan lamarin, kodayake mutane da yawa sun samu rauni.”