✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar bututun mai ya kashe mutum 17 a Legas

Hukumomi a jihar Legas sun ce akalla mutum 17 ne suka mutu kuma da dama suka jikkata sakamakon fashewar bututun mai a unguwar Abule Ado…

Hukumomi a jihar Legas sun ce akalla mutum 17 ne suka mutu kuma da dama suka jikkata sakamakon fashewar bututun mai a unguwar Abule Ado da ke yankin Festak a karamar hukumar Amuwo Odofin a jihar Legas.

A cikin wadanda suka rasu akwai faransipal da wasu daliban makarantar sakandaren kwana.

Jama’ar yankin sun gobarar ta tagayyara sama da gidaje  50 tare da motocin da suka ci wuta.

“Mutum 17 ne aka tabbatar da mutuwar su yayin da 25 suka samu mummunan raunuka sanadiyyar gobarar,” Kamar yadda gwamnatin jihar Legas ta wallafa a shafinta na Twitter.

Wata biyu da suka wuce an sanu irin wannan gobarar a cikin garin Abule Egba, inda mutum biyu suka mutu yayin da sama da jama’a 300 suka rasa gidajensu.

Lokacin da gobarar ke ci