Sakamakon fasa rumbunan abinci da matasa suka yi a sassan Jihar Adamawa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya dokar hana fita na awanni ashirin da hudu.
Da yake sanarwar da ke cewa dokar za ta fara aiki daga karfe 3 ranar Lahadi, Fintiri ya ce rashin dakatar da barnar na iya janyo asarar rayuka da na dukiyoyin jama’a.
“Na sanya dokar hana fita daga safiya zuwa yamma daga karfe 3 na rana na Lahadi, 25th ga watan Oktoba, 2020.
“Ba za mu amince da zirga-zirgar kowace mota ba illa motocin da aka amince musu su yi zirga-zirga.
“A matsayinmu na gwamnati dole ne mu yi iya kokarinmu domin kare hakkin jama’a sannan ba za mu amince da karya doka ba kowace iri ce.
“Jama’a da su natsu kuma su kwantar da hankulansu har tsawon lokacin da muka gama dakatar da lamarin”, inji shi
Gwamnan ya jinjina wa matasan da suka kame kansu a lokacin zanga-zangar #EndSARS sannan ya dau alkawuran kare hakkin kowa a jihar.