✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fargabar kai hari ta sa dalibai zana jarrabawa 13 a yini guda a Abuja

An tilasta daliban da su rubuta jarrabawar darussa 13 cikin wuni daya.

Fargabar kai harin ‘yan ta’adda a wasu makaratu a Abuja, ta tilasta gudanar da jarrabawar gaggawa ga dalibai tare da rufe makaratun a Talatar nan. 

Wasu daliban makarantun sakandare na jeka ka dawo da Aminiya ta zanta da su, sun bayyana yadda suka zana jarrabawar darusa 13 daban-daban a yini guda.

Haka kuma, daliban wasu makarantun kwana sun soma zana jarrabawar wasu darrusa tun a daren ranar Litinin.

Wani shugaban makarantan sakandare a Kubwa, ya ce sun fara gudanar da jarrabawar ga dalibai a ranar Alhamis din da ta gabata.

Sai dai ya ce har zuwa ranar Litinin, jarrabawa uku kawai daliban suka yi kasancewar ana yi musu jarrabawar darasi guda daya ce duk yini.

“Sai dai bayan umarnin da mahukunta suka bayar na lallai sai mun kammala dukkan jarrabawar a yau [Talata], dole ta sa muka yi musu jarrabawar darusa 13 a yau kadai.”

Ya ce daliban sun kammala zana jarrabawar darussan 13 da Yammacin Talata, kuma nan take suka umarci dalibai da su tafi gidajensu.

Mun ga tasku a wajen rubuta jarrabawa —Dalibai

Dalibai da dama da Aminiya ta zanta da su, sun bayyana irin wahalar da suka sha yayin rubuta jarrabawar.

Daliban wadanda wasu daga cikinsu ke zuwa makarantun daga yankuna masu nisa, sun ce sun zo makaranta ne ba tare da shirin abin da za su ci da rana ba, kuma ba a basu lokacin komawa gidajensu don cin abinci ba.

“Hakan ya sa wasu daga cikinmu sun jigita matuka kasancewar ruwa muka yi ta sha saboda yunwa kuma babu abin da za mu ci,” in ji daya daga cikin daliban.

Sun kuma koka da matsalar da suka fuskanta a yayin rubuta jarrabawar a sakamakon rashin yin cikakken karatu a kan darusan da kuma halin fargaba da suka samu kansu a ciki.

Wata daliba a makarantar sakandare ta kwana ta ‘yammata da ke Dutse-Makaranta a Abuja da iyayenta suka daukota daga makarantar, bayan samun sako na bukatar hakan a ranar ta Talata, ta ce an shirya musu jarrabawa biyu a ranar Litinin da su ka fara da misalin karfe tara na dare, sannan suka ci gaba da yin jarrabawar a safiyar Talata.

Aminiya ta ruwaito cewa, umarnin rufe makaratun ya shafi na firamare da sakandare na gwamnati da kuma masu zaman kansu da ke Abuja.