✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Soludo ya lashe zaben gwamnan Anambra

Farfesa Charles Soludo ya samu kuri'u mafiya rinjaye bayan kammala zaben

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, a matsayin zababben gwamnan Jihar Anambra.

Jami’ar Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Florence Obi, ta ce Farfesa Soludo ne ya samu kuri’u mafiya yawa, sannan ya cika dukkan ka’idojin da ake bukata.

“Ni Farfesa Florence Obi, a matsayina na Jami’ar Tattara Sakamkon Zaben Gwamnan Anambra da aka gudanar a ranakun 6 da 9 ga watan Nuwamba, ina tabbatar da cewa an yi zabe kuma Farfesa Charles Soludo ne, bayan ya cika dukkan sharuddan da ake bukata, ya lashe zaben”, inji ta.

Farfesa Soludo, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya lashe zaben ne da kuri’a 112,229, lamarin da ya sa ya bai wa mai biye mishi, dan takarar jam’iyyar PDP Chief Valentine Ozigbo, tazarar kuri’a 58,422.

Inconclusive

Ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba ne dai aka gudanar da zaben na gwamnan Jihar Anambra, amma saboda soke wasu kuri’u da aka yi a Karamar Ihiala, INEC ta ayyana zaben da cewa inconclusive ne, wato bai kammala ba.

Ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba aka kammala zaben, sannan aka samu sakamakon da ya nuna jam’iyyar APGA ta yi nasara da gagarumin rinjaye.

Sakamakon zaben dai ya nuna Farfesa Soludo ne ya lashe dukkan kananan hukumomin jihar idan aka cire guda biyu wadanda ‘yan takarar PDP, Valentine Ezigbo, da YPP, Ifeanyi Uba, suka tsira da su.

Wata bajintar da Farfesa Soludo ya yi kuma ita ce dada ’yan takarar APC da PDP da kasa a Karamar Hukumarsu ta asali, wato Aguata – dukkan manyan ’yan takarar  uku daga Karamar Hukumar Aguata suka fito.

Jam’iyya mai mulki a Najeriya, wato APC, ba tu samu ko da karamar hukuma daya ba.

Ita dai APC ta samu kuri’a 43,285 ne yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta samu 53,807.

Jam’iyyar YPP, wadda ta kwaci karamar hukuma daya da kyar, ta tashi da kuri’u 21,261.