Hukumomin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (Unizik) da ke, Awka a Jihar Anambra ta kori ɗalibar nan mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cin kwalar wani malamin jami’ar Dakta Chukwudi Okoye.
A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga Goddy-Mbakwe ta far wa malamin jami’ar, Dakta Chukwudi bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani wuri da ke harabar jami’ar.
A cikin takardar korar ɗalibar da jami’ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wanda muƙaddashin magatakardar jami’ar, Ɓictor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin korar ne bayan shawarar kwamitin bincike da jami’ar ta yi.
Hukumar jami’ar ta ce ”Kwamitin ya samu ɗalibar da laifin saɓa wa dokokin ladabtarwa na jami’ar, musamman sashe na 4 na dokar ladabtarwa ta (SDR)”, in ji takardar korar.
Bidiyon cin kwalar malamin ya ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta kiraye-kirayen ɗaukar mataki kan lamarin.
Hukumar Jami’ar ta buƙaci ɗalibar da ta gaggauta ficewa daga harabar jami’ar tare da mayar wa jami’ar duk wasu abubuwan da ke hannun ɗalibar.