✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Nur Alkali da Alhaji Garba A.D. sun rasu

A cikin kwanakin bakwai da suka gabata yankin Arewa ya sake rasa wasu daga cikin fitattun ’ya’yansa biyu wato Farfesa Muhammad Nur Alkali daya daga…

A cikin kwanakin bakwai da suka gabata yankin Arewa ya sake rasa wasu daga cikin fitattun ’ya’yansa biyu wato Farfesa Muhammad Nur Alkali daya daga cikin wakilai shida na Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (SCIA) da kuma fitaccen dan kasuwan nan basarake Alhaji Garba AD Inuwa Talban Kano.
Farfesa Alkali ya rasu ne a gidansa da ke Maiduguri a cikin dare ranar Juma’ar da ta gabata yana da shekara 68.
Farfesa Alkali wanda farfesan tarihi ne ya taba zama Shugaban Jami’ar Maiduguri har sau biyu daga 1985 zuwa 1992, kafin ya zama Daraktan Cibiyar Bincike da Tsara Dabarun kasa (NIPSSS) da ke Kuru, Jos Jihar Filato. Kuma ya zama shugaban kwamitin ba Shugaban kas shawara a zamanin Janar Abacha, sannan a baya-bayan nan ya kasance wakilin kwamitin Shugaban kasa kan matsalar tsaro a Arewa maso Gabas kwamitin da ake kira na sulhu da Boko Haram.
An yi jana’izarsa a ranar Asabar a Maiduguri, inda gwamnati da fitattun jama’a suka rika aikawa da sakonnin ta’aziyya ga iyalai da jama’ar jihar Borno kan wannan babban rashi.
Farfesa Alkali shi ne wakilin kwamitin taron kasa na hudu da ya rasu, sauran wadanda suka rasu sun hada da marigayi Hamma Misau (da ke wakiltar manyan jami’an ’yan sanda masu ritaya) wanda ya fito daga Jihar Bauchi wanda ya rasu ranar 27 ga Maris, sai Muhammad Jumare daga Jihar Kaduna wanda ya rasu ranar 5 ga Mayu, sai kuma Dora Akunyili daga Jihar Anambra wadda ta rasu ranar 7 ga Yuni.
 Shi kuwa Talban Kano Alhaji Garba AD Inuwa ya rasu ne a ranar Talata da daddare bayan doguwar jinya.
Marigayi Garba AD yana daga cikin fitattunn’yan kasuwa a shekarun 1970 zuwa 1980 a tsohuwar Jihar Kano.
An yi jana’izar marigayin a shekaranjiya Laraba a kofar Kudu ta fadar Mai martaba Sarkin Kano, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi ll da Alhaji Nasiru Aliko Koki da Hakiman Sarkin Kano da dimbin jama’a suka halarci Sallar jana’izarsa.
Marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya da dama cikinsu har da Alhaji Auwalu Garba wani dan kasuwa mazaunin birnin Landan a kasar Ingila.