✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Asabe Kabir: Tawakkali na rage saurin tsufa

Farfesa Asabe Kabir, lakcara ce a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. Ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha a wajen neman ilimi. Ta bukaci…

Farfesa Asabe Kabir, lakcara ce a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. Ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha a wajen neman ilimi. Ta bukaci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi. Ta ce tawakalli shi na rage zuwan tsufa.

Tarihina
Assalamu alaikum, sunana Asabe Kabir, ni ce ’ya ta bakwai a wurin mahaifinmu Alhaji Abdulkareem Lafene daga karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja. Na girma a wurin Kawuna Alhaji A. S. Muhammad. Na fara makarantar firamare a Capital School da ke Sakkwato a shekarar 1972, bayan an kirkiro Jihar Neja a 1976 sai na ci gaba a Capital School da ke garin Minna. A shekarar 1978 ne na shiga Kwalajen Gwamnatin Tarayya ta ‘Yan mata da ke Oyo, sannan na kammla a shekarar 1983. Daga nan sai na samu shiga Jami’ar Sakkwato, wadda a yanzu ake kiran ta Jami’ar Usman danfodiyo. Inda na yi digiri a fannin Turanci, wato a shekarar 1988 ke nan.
Na yi koyarwa na shekaru kadan, sannan na sake koma wa Jami’ar Usman danfodiyo a shekarar 1999, inda na yi digiri-na-biyu a kan Adabin Turanci (English Literature). Bayan nan na yi Difloma ta Musamman a kan Koyarwa a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato.
Na koyar makarantun sakandare masu yawa da ke jihohin Sakkwato da Zamfara. Na koyar a Halliru Binji College of Arts and Science wadda a yanzu ta dawo Sokoto Polytechnic. Daga bisani na koma sashin yarukan kasashen turawa da ke Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato a shekarar 1998, inda na fara a matsayin lakcara mai matsayi na biyu.
Daga nan na rike mukamai masu yawa inda a watan Oktoba, 2010 na zama Farfesa a bangaren Adabin Baka da kuma Adabin Afrika, an tabbatar mini a ranar 25 ga watan Mayu, 2013.
Abin da ba zan mantawa da shi ina karama ba
Nakan tuna yadda na gudanar da rayuwata a cikin ’yan uwana, na yi rayuwata cikin farin ciki da jin dadi.  
Yadda na ji bayan na zama uwa
Na kasance cikin yanayin farin ciki na musamman bayan na zama uwa. Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya biyu mata. Fadila, ta kammala digiri a fannin Tsimi da Tanadi da kuma Firdausi da ta yi digiri a fannin aikin lauya. Dukkansu sun yi aure.  Kun ga wannan ba karamar baiwa ba ce. Na gode wa Allah (SWT).           
Burina ina karama
A lokacin da nake makarantar firamare burina in zama matukiyar jirgin sama. A lokacin da nake sakandare kuma sai na ci burin zama lauya. Ban fitar da ran zama lauya ba har sai da na shiga jami’a, inda kaddara ta sanya na yi digiri a yaren Ingilishi, na kuma yi digiri na biyu a bangaren Adabin Turanci, sannan na zama lakcara. Duk da haka cewa burina in zama lauya ko matukiyar jirgi amma ban taba nadamar kasancewata lakcara ba.
Nasarori
Babbar nasara da na cim ma shi ne iyalina sun kasance cikin farin ciki, na kuma cim ma nasara a bangaren karatu da aiki da kuma sauran batutuwa rayuwa.
Matan da na so kwaikwaya lokacin ina karama
A duk lokacin da na ga wata mata ta shahara wajen wani aiki duk da irin kalubalen da mata suke fuskanta sai na ji tana burge ni, hakan ya sanya na tsaya kai da fata wajen ganin na cim ma burina duk wani abu da na sanya a gaba.
Yadda nake hada aikina da lura da iyali
A kowane lokaci nakan fi ba da aurena muhimmanci fiye da komai a rayuwata, hakan ya sanya ba na wasa da ayyukan gida kuma su ne a farko. Kodayake ban sha wahala wajen lura da ’ya’yana ba, kasancewar a lokacin da suke kanana ba ni da ayyuka masu yawa, don haka sai na samu damar lura da mijina da kuma ’ya’yana cikin sauki da kwanciyar hankali. A lokacin da ’ya’yana suke girma sai na ba su kyakkyawar tarbiyya inda suka zama nagari. Na shaku da su, inda na zama tamkar babbar kawarsu. Ban yarda aikina ya nisanta ni da iyalina ba. Na kuma samo dabarun lura da iyalina ba tare da aikina ya shafi hakan ba. Mijina ya taimaka mini ta wannan bangaren. Ina gode masa.
Abin da nake so a tuna ni da shi idan ba na nan
Ina so a tuna ni a matsayin mai gaskiya da za a iya yarda da ita a kowane irin hali, sannan ina so a tuna ni a matsayin mai bin ka’idoji. Ina so a tuna ni a matsayin mace tagari da ba ta cuci kowa ba, wadda ta kasance mai taimakon jama’a a kowance lokaci.
Sirrin rashin bayyanar tsufata
Tabbas na kusan cika shekara 50, amma idan an gan ni ba za a taba yarda na kai haka ba, sirrin rashin bayyanar tsufata shi ne, kullum ina cikin farin ciki da tawakkali. Idan mutum ya kasance cikin farin ciki, to zai samu natsuwa, inda hakan kuma sai sanya jikinsa ya sake. Kun san damuwa da yawan tunani ne suke bayyanar da tsufa, to ba na bari in kwana da damuwa.
Babban darasin da na koya
Na koyi darasin babu ta yadda dan Adam zai iya gamsar da kowa-da-kowa. Duk adalci da taimako da kyautatawarka, kuskure daya ka yi sai a manta da duk ayyukan alheran da ka yi. Babu abin da ya dame su da cewa kuskure aka samu, abin da ya dame su shi ne, a kullum ka yi musu abin da zai dadada musu. Daga nan sai na koyi in rika yin abin da ya dace ba tare da tsoro ko abin da mutane za su ce ba. Na kuma koyi darussa daga kura-kuran da na aikata da kuma wadanda wadansu suka aikata.
Wuraren da na fi son ziyarta
Na je wurare da dama, amma nakan so na je wurin da zan koyi wani abu da zai amfane ni a rayuwa.
Abincin da na fi so
Duk wani abinci da yake Halal.
Shawara ga mata
Kowace mace za ta samu nasara ta hanyar jajircewa a kan duk wani abu da ta sanya a gaba, musamman ma idan za ta iya shawo kan matsalolin da mata ke fuskanta a cikin al’umma.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da mijina ne a makon farko da shiga garin Sakkwato karatu a shekarar 1983 ke nan.
Babbar kyauta daga mijina
Babbar kyauta daga mijina ita ce, soyayyar da ya nuna mini, wanda hakan ya sanya muka samu zaman lafiya, bugu da kari ya taimaka mini da duk wani abu da nake bukata a rayuwa. Ya ba ni kyautar kwarin gwiwa a duk wani abu da zan yi.
kalubale a matsayina ta mace Farfesa
Ban fuskanci kalubale mai yawa ba. Na jajirce wajen duk abin da nake yi, kuma iyalina sun taimaka mini a duk lokacin da nake bukatar taimako. ‘Yan uwa da abokan arziki ma sun taimaka mini sosai, hakan ya sanya na shawo kan duk wani kalubalen da ya ci mini tuwo a kwarya.
Halayen da na fi so
Ina so mutum ya kasance mai tarbiyya, mai kuma aikata komai a kan ka’ida. Ba na so mutum ya rika aikata abin da ya saba wa shari’a da al’ada.
Ranakun farin ciki bayan na zama uwa
Ranar da na aurar da ’ya’yana da kuma ranar da na samu jikina na farko.
Yadda nake hutawa  
Nakan huwta ne a cikin iyalina, a nan zany i hira wadda hakan ke sanya ni natsuwa da kwanciyar hankali.  
Tufafi
Na fi son tufafi na al’ada, ba mai dauke da ado rambatsau ba.

sai na koyi in rika yin abin da ya dace ba tare da tsoro ko abin da mutane za su ce ba. Na kuma koyi darussa daga kura-kuran da na aikata da kuma wadanda wadansu suka aikata.
Wuraren da na fi son ziyarta
Na je wurare da dama, amma nakan so na je wurin da zan koyi wani abu da zai amfane ni a rayuwa.
Abincin da na fi so
Duk wani abinci da yake Halal.
Shawara ga mata
Kowace mace za ta samu nasara ta hanyar jajircewa a kan duk wani abu da ta sanya a gaba, musamman ma idan za ta iya shawo kan matsalolin da mata ke fuskanta a cikin al’umma.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da mijina ne a makon farko da shiga garin Sakkwato karatu a shekarar 1983 ke nan.
Babbar kyauta daga mijina
Babbar kyauta daga mijina ita ce, soyayyar da ya nuna mini, wanda hakan ya sanya muka samu zaman lafiya, bugu da kari ya taimaka mini da duk wani abu da nake bukata a rayuwa. Ya ba ni kyautar kwarin gwiwa a duk wani abu da zan yi.
kalubale a matsayina ta mace Farfesa
Ban fuskanci kalubale mai yawa ba. Na jajirce wajen duk abin da nake yi, kuma iyalina sun taimaka mini a duk lokacin da nake bukatar taimako. ‘Yan uwa da abokan arziki ma sun taimaka mini sosai, hakan ya sanya na shawo kan duk wani kalubalen da ya ci mini tuwo a kwarya.
Halayen da na fi so
Ina so mutum ya kasance mai tarbiyya, mai kuma aikata komai a kan ka’ida. Ba na so mutum ya rika aikata abin da ya saba wa shari’a da al’ada.
Ranakun farin ciki bayan na zama uwa
Ranar da na aurar da ’ya’yana da kuma ranar da na samu jikina na farko.
Yadda nake hutawa  
Nakan huwta ne a cikin iyalina, a nan zany i hira wadda hakan ke sanya ni natsuwa da kwanciyar hankali.  
Tufafi
Na fi son tufafi na al’ada, ba mai dauke da ado rambatsau ba.