✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfado da soyayya cikin rayuwar ma’aurata (4)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan abubuwan da ke suke nakasa so da kauna a tsakanin ma’aurata:

Dabi’un mata masu dakushe soyayya

 

1.  Raini da rainuwa

Nan da nan suke bice soyayyar uwargida daga cikin zuciyar maigida, in ma aka yi dace da namiji marar hakuri, sai abin ya kai har ga mutuwar aure. Yawancin mata na fama da dabi’ar raina kokarin da mazansu ke yi a kansu, wadansu kuma komai irin kyautatawar da mijinsu ya yi musu, dan karamin laifi sai ya goge wannan kyautatawar ta shekaru da yawa. Wannan hali shi ke kai da yawan matan wannan al’umma cikin wutar Jahannama kamar yadda Hadisin Manzon Allah (SAW) ya bayyana mana. ’Yan uwa mata mu sani, gaskiya duk macen da ta raina mijinta, ba ta kunyar harararsa ko yi masa tsaki; ba ta kunyar gaya masa bakaken maganganu, to wannan matar ba albarka a tare da ita, domin ta dauki wata dabi’a ta ’yan wutar Jahannama. To yaya za a yi kuwa ta kasance cikin albarka?

Maganin haka shi ne, uwargida ki sani, mijinki ko rainanne ne, ko wawa ne, ko shi ke yin abin da ke jawo masa rainin, in dai mijinki ne, to ya wuce raini a wajenki. Ki tuna fa shi ne rabin addini ne gaba dayansa, hanyar shiga aljannarki ce, to in kin wulakantata, kin raina ta kina zaton za ta bude miki balle ki shiga?

Maigidanki shi ne sarkinki, gwamnanki, ya ma fi duk wani sarki ko gwamna matsayi a wurinki. Haka kuma ya fi mahaifinki matsayi in dai kina aurensa, to ba ki iya raina sarkin garinku ko mahaifinki sai shi da duk ya fi su matsayi ya kamata a ce kin raina shi? To yaya albarka za ta kasance a tare da mai raina mijinta?

Uwargida ta kasance mai karramawa da jinjinawa da kambama mijinta a koyaushe, wannan na raya soyayyarki cikin zuciyar mijinki.

Kuma ko yaya maigidanki yake da wuyar hali, ki dage da yi masa ladabi da biyayya da karramawa da kyautatawa; domin in kin tuna, ai ba don shi kike yi ba, don Allah kike yi, ibada ce kike yi domin gyarar lahirarki; Allah ne Ya ce ki yi masa haka, kuma Shi Zai ba ki lada. Duk wata hararar da za ki yi ga maigidanki ta kasance ta soyayya ce ba ta wulakanci ba, duk wani murgudawa da zobara baki ya kasance na wasa ne ba na raini ba.

 

2.  Haihuwar fari

Da mace ta yi haihuwar fari, sai soyayya da kulawarta ga mijinta su ragu sosai su koma kan sabon jaririnta, yanzu shi ke cinye duk lokacinta, ya fi muhimmanci gare ta da mijinta, sai ta rage tarairayarsa ta yi ta tarairayar sabon jaririnta. Yawanci wannan rage nuna soyayyar da tarairayar shi ke sa maza karin aure, domin duk abubuwan da jariri ke so; na tarairaya, yawan kulawa, nuna kauna da soyayya, ba shi lokaci da muhimmanci sama da komai, shi ma maigida koyaushe cikin bukatarsu yake, in an daina yin su gare shi, dole ne ya yi begensu, don haka nan da nan kwakwalwarsa za ta fara raya masa bukatarsa karin aure don ci gaba da dandana wadancan zakakan abubuwa.

Maganin haka shi ne, duk da yake soyayyar uwa ga danta ta shafe kowace irin soyayya da ke cikin zuciya, amma yana da kyau uwargida ta auna da dan nan da shiga Aljannar rahma wanne ya fi muhimmanci a gare ta? Kin ga dai danki ke zai bi ya samu shiga Aljanna; ke kuma sai kin bi mijinki ki shiga Aljanna; ba biyayyar da ta kai kyutatawa da nuna soyayya.

Ba wani hukunci na azabtarwa da za a yi ga uwar da ba ta ba danta cikakkiyar kulawa, asali ma, a cikin Alkur’ani Mai girma, Allah (SWT) Yana cewa:

“…Ba a cutar da uwa game da danta kuma ba a cutar da uba game da dansa…”

Amma akwai hukuncin, cewa ba Aljanna ga macen da ba ta kyautata wa mijinta.

A nan ba wai ina nufin a bari ko a rage kula da yara a koma ga miji kadai ba ne, ina dai son uwargida ta fahimci cewa maimakon jariri daya, to yanzu jariranta sun zama biyu, domin maigida shi ma wani babban jariri ne, duk wata kulawa da tarairaya da nuna soyayya da wasa da dariya, to shi ma yana bukatarsu, sai a dage wajen ganin an daidaita, kada a yi watsi da maigida gaba daya don zuwan sabon jariri.

 

3.    Kazanta

Tsabta da kwalliya da gyaran jiki na da matukar muhimmanci wajen rayar da soyayya da kara dadin zamantakewa a tsakanin ma’aurata. Wata sa’ar karuwar iyali da sauran al’amura na yau da kullum kan sa mace da ba kazama ba ta zama kazama. Shawara a nan ga uwargida ita ce kada ta bari ayyuka su rika taruwa mata, duk aikin da ya taso a yi shi take-yanke ba tare da jinkiri ba, ta haka sai a ga an kiyaye tsabtar.

Sannan lokacin shayarwa, uwa ta kiyaye da karnin nono da na tumbidi, kada uwargida ta yi sabo da su ya kasance har sun bi jikinta, ita ba ta ji sai dai in an kusance ta a ji. To yaya maigida zai so kusantarki bayan kina wari mai sa kyankyamin a zuci? Sai a riki dabia’ar sa turare koyaushe, In ma ba halin sayen turare, a rika matsa lemun tsami cikin ruwan wanka, haka goga lemun tsami a hammata na rage warin hammata.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawawarSa a koyaushe, amin.