Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin da ma’arata za su bi don farfado da so da kauna da inganta zamantakewa a tsakaninsu:
In muka lura da yanayin zamantakewar auratayya a wannan zamanin, za mu ga cewa yawanci zaman hakuri kawai ake yi ba zaman so da kauna da jiyar da juna dadi da taimakon juna ba. Da yawa mukan ji wadansu ma’aurata na cewa ai ba wata soyayya sai dai zaman hakuri ko a ce ana zaune ne domin yara kawai, alhalin in aka duba tarihi akwai lokacin da ma’aurata suke cikin tsananin soyayyar juna har suna jin ba abin da zai iya shafe soyayyarsu har abada. Amma a hankali sai su wayi gari su nemi wannan soyayya a tsakaninsu su rasa.
Ga ma’auratan da ke juyayin ina soyayyarsu ta lokacin samartaka ko lokacin amarci take; su sani cewa wannan soyayyar tana nan, illa dai kurar canje-canje ta rayuwa da ta lullube ta kuma ta dusashe kaifinta. Wannan bayani in Allah Ya so zai karantar da ma’aurata yadda za su kakkabe duk wata kura da ta boye soyayyarsu da yadda za su wasa kaifinta da kara zafafa ta har tafi ta da ma dumi. Ga wadanda soyayyarsu na nan da duminta, bayani zai zo kan yadda za su kara tabbatar da wannan dumi har karshen rayuwarsu cikin yardar Allah Azza Wa Jallah!
Sinadarai uku na aure:
Yana da kyau ma’aurata su san cewa Allah (SWT) Ya gina zamantakewa irin ta auratayya a kan sinadarai uku: natsuwa, soyayya da tausayi (jinkai) kamar yadda Ya sanar mana a cikin Alkur’ani Mai girma:
“Kuma daga cikin ayoyinSa shi ne Ya halitta muku mata daga kawunanku, domin ku samu natsuwa daga gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku; lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga ma’abota tunani.”
Ga bayani kan sinadaran nan uku da tasirinsu a rayuwar aure:
Natsuwa:
Aure yana samar da natsuwa a rayuwar ma’aurata da dama: na farko akwai samar da natsuwa ta sha’awar mutum, duk ma’aurata suna da natsuwar cewa duk lokacin da sha’awarsu ta motsa, to fa suna da wannan na musamman din da zai biya musu bukata cikin kwanciyar hankali kuma duk lokacin da suka so.
Akwai kuma samun natsuwar cewa mutum yana da wani na musamman da Allah Ya kaddara shi ne kamar wani murufi da ya rufe gibin rayuwarsa, wanda da shi zai cika masa addininsa, wanda zai boye masa sirrinsa, zai taimake shi ya rufa masa asiri a duk lokacin da wata masifar rayuwa ta taso, kamar yadda Allah (SWT) Ya fada mana cikin Suratul Bakara, aya ta 187:
“….Su (matan aurenku) tufa ne a gare ku, kuma tufa ne a gare su…”
Akwai kuma samun natsuwar cewa mutum yana da wannan na musamman da yake jin dadin zama da shi, wanda zama da shi yake kayatar da shi fiye da zama da kowa a duniya, kamar yadda Allah (SWT) Ya nuna cikin Suratul A’araf, aya ta 189 cewa Ya halicci mace daga cikin namiji, domin ya ji dadin zama da ita.
“Shi ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma daga gare shi Ya halitta matarsa domin ya ji dadin zama da ita” K:7: 189
Ga namiji akwai samun natsuwar cewa ko ina ya je ya dawo, yana da wannan ta musamman da za ta kula da shi, ta tarbe shi cikin murya mai taushi, ta rirriga shi ta hutar da shi. Ga mace kuma akwai samun natsuwar cewa tana da wani mai ciyarwa, shayarwa da tufatar da ita da kuma tsare mata mutuncinta da kare ta daga duk wani abu da zai cutar da ita. Da dai sauran natse-natse iri-iri da sukan iya dangantaka da yanayin ma’aurata da yanayin aurensu.
Soyayya:
Natsuwa ita ke haifar da soyayya ta ainihi kuma tabbatacciya, ba irin soyayyar saurayi da budurwa ba, wacce yawanci soyayya ce da sinadaran jinsi na sha’awa da kuma sinadaran shauki ke haifarwa, amma soyayyar rayuwar aure daban take, domin ita Allah (SWT) ke kafa ta cikin zukatan ma’aurata kamar yadda ya zo a cikin ayar da ke sama.
Tausayi:
Soyayya kuma ita ke haifar da tausayi, har ya kasance mutum na hakuri da nakasun abokin zamansa da kau da kai ga abin da inda wani ne ya yi masa shi, to sai an kai ruwa rana. Mace sai ya kasance tana hakuri da rashin samun mijinta ko miji ya yi hakuri da wuyar halin matarsa da sauransu.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.