Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya kayyade farashin man fetur a kan Naria 138 da kobo 62.
Bisa umarnin na NNPC, daga yanzu masu manyan rumbunan man fetur za su rika ba wa dillalai masu sari kowace litar mai a kan N138.62.
Dillalan za kuma su rika sayen kananzir a kan Naira 160 kowace lita.
Manajan Kasuwanci a kamfanin sayar da albarkatun mai na NNPC (PPMC), Mohammed Bello a cikin sanarwa ya ce sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar Laraba 5 ga watan Agusta 2020.
Danarwar ta kara da cewa za a rika sayar wa su masu manyan rumbunan mai kowace litar man fetur a kan Naira 113 da Kobo 70.
Man gas kuma za a rika ba su kowace lita a kan N160 a Legas, a Oghara kuma a kan N165.
Sia dai har yanzu hukumar kayyade farashin albarkaun mai (PPPRA) ba ta fitar da mizanin farashin da gidajen za su rika sayarwa ga masu ababen hawa ba.