Manoman tumatir da tattasai a garin Bula da ke ƙaramar hukumar Akko a Jihar Gombe, na fuskantar matsananciyar asara sakamakon faduwar farashin tumatir da ya yi ƙasa da kashi 90 cikin makonni biyu kacal.
A yayin wata ziyarar da wakilinmu ya kai kasuwar Bula ya lura da dubban kwandunan tumatir da buhunan tattasai a kasuwar suna jiran masu siye, amma manoman na fama da rashin samun kwastomomi duk da ƙarancin farashin.
- Yadda mafi lalacin kulob ya yi nasara ɗaya cikin shekara 20
- Mutum 32 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Zamfara
Farashin babban kwandon tumatur, wanda ake siyarwa a kan N10,000 makonni biyu da suka wuce, yanzu ya fadi zuwa N1,000 kacal.
Farashin tattasai ma ya ragu sosai, inda buhu ɗaya yanzu ake sayarwa akan N10,000, sabanin N40,000 makonni biyu da suka gabata, wanda ya zama ragin kashi 75 cikin 100.
Farashin attaruhu ma ya fadi da kashi 68, inda buhu ɗaya yanzu ake sayarwa akan N16,000 maimakon N50,000 da aka saba sayarwa.
Alhaji Saleh Maikudi, Shugaban Ƙungiyar Manoman Tumatur a garin Bula, ya bayyana cewa manoman na samun gagarumar asara kowacce rana.
A cewarsa, suna rasa N9,000 a kowane kwandon tumatir, N30,000 a kowanne buhun tattasai, da kuma N34,000 a kowanne buhun attaruhu (albishir) idan aka kwatanta da farashin makonni biyu da suka gabata.
Manomin mai shekaru 35 ya koka cewa faduwar farashin da aka samu ta tilastawa manoma roƙon kwastomomi su sayi amfanin gonar su, suna fargabar asarar amfanin gona idan aka ci gaba da wannan hali.
“Muna roƙon Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Jihar Gombe su taimaka mana ta hanyar samar da masana’antu na sarrafa kayan amfanin gona don rage asarar bayan girbi.
“Idan muka samu damar sarrafa tumatir da tattasai da muke da su, za mu kaucewa ƙarancin da aka fuskanta watanni kaɗan da suka wuce,” inji Maikudi.
Shi ma Malam Khalifa Bello, Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Kayan Lambu, ya nuna damuwa game da asarar kuɗi da ake yi.
Ya yi kira ga Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe da masu zuba jari na ɓangaren masu zaman kansu da su tallafa wa manoma ta hanyar samar da ƙananan masana’antu na sarrafa tumatir don juya ragowar tumatir ɗin zuwa man tumatir ko gari, wanda za a iya adanawa kuma a sayar da shi daga baya.
Bello ya bayyana cewa faduwar farashin ya faru ne saboda yawan tumatir da tattasai da ake girba lokaci guda, kasancewar manoma yanzu haka suna tsakiyar lokacin girbi.
Ya ƙara da cewa sama da kwanduna 1,500 na tumatir da buhunan tattasai 2,000 ke barin Bula zuwa sassa daban-daban na Nijeriya a kullum.
Kwanaki huɗu da suka wuce, ana sayar da kwandon tumatir akan N150,000, wanda hakan ya nuna banbancin babba a kasuwar.