Farashin tumatir da tattasai da albasa ya fadi warwas a kasuwannin Jihar Taraba, a jajibirin Karamar Sallar wannan shekara.
Wannan shi ne karo na farko a tsawon lokaci da aka sami faduwar farashin kayan miya haka a lokacin da ake tsaka da shirin bukukuwan Sallah.
- Mutum 80 sun mutu a turereniyar karbar kayan Sallah
- Gidauniya Ta Dinka wa Marayu 103 Kayan Sallah A Gombe
Binciken Aminiya ya gano farashin kayan tattasai ya fadi warwas a Kasuwar Jalingo inda yanzu buhun tattasai mai nauyin kilo garam 50 ya koma Naira dubu shidda daga dubu tara.
Farashin kwandon tumatir ya fadi daga Naira dubu biyar zuwa Naira dubu uku, sai buhun albasa daga dubu biyar ya koma dubu biyu da dari biyar.
’Yan kasuwan da wakilin Aminiya ya zanta da su sun bayyana cewa sun yi asarar Naira dubu biyu akan kowane buhu ko kwando na tumatir da tattasai.
Daya daga cikinsu mai suna Garba Hudu ya ce daga jihohin Bauchi da Jigawa da Katsina suke sayo kayan miya suna kawowa Jihar Taraba domin neman riba.
Ya ce farashin kayan miya ya fadi sosai a Kasuwar na Jalingo wanda an dade ba a sami irin haka ba a lokacin bukukuwan Sallah.