A yayin da farashin hatsi ke ci gaba da tashin gwaron zabo a sassan Najeriya, farashin kayan gwari kuwa, da ya kasance da matukar tsada a kwanakin baya, yanzu farashinsa ya fadi kasa warwas a Kasuwar Tumatur da ke Farar Gada Jos, Jihar Filato.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a wannan kasuwa, ya gano cewa buhun albasa da ake sayarwa a watan Disambar bara Naira 70,000, yanzu ya koma Naira 6,000.
Hakazalika babban kwandon tumatur da ake sayarwa kan Naira 8,000, karaminsa kuma ake sayarwa Naira 5,000 a bara, yanzu ya koma babban kwando Naira 2,000; a yayin da karamin ya sauka zuwa Naira 1,000.
Buhun tattasai da ake sayarwa kan Naira 15,000 a da, yanzu shi ma ya fadi zuwa Naira 4,000.
Buhun solon tarugu da ake sayarwa a da kan Naira dubu 15,000, yanzu ya fado zuwa Naira 3,000.
A yayin da buhun shambo da ake sayarwa kan Naira 11,000, shi ma ya fado zuwa Naira 3,000.
Da yake zantawa da wakilinmu, kan wannan al’amari na faduwar farashin kayayyakin, Mataimakin Shugaban Kasuwar ta ’Yan Tumatur ta Farar Gada Abdullahi Yusuf, ya bayyana cewa na farko abin da ya kawo saukar farashin kayan, shi ne kayayyakin gwari na rani sun fito. Kuma masu sayen kayan babu kudi a wajensu.
Ya ce wannan shi ne ya kawo faduwar kayan gwari a wannan lokaci.
Ya ce duk da faduwar farashin kayan, amma babu ciniki saboda halin da ake ciki na rashin kudi.
“A bara a daidai wannan lokaci, kullum muna samun masu sayen kayan da suke loda motocin J5 sama da 10 amma a bana ko motoci 3 ba mu iya lodawa na kayan da aka saya.
“Saboda bana baki masu zuwa sayen kaya, sun yi karanci a wannan kasuwa.
“A shekarun baya a duk Najeriya, babu jihar da ba su zuwa sayen kaya a wannan kasuwa.
“Amma yanzu daga Fatakwal ne kadai suke zuwa sayen kaya a wannan kasuwa.”
Ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Shehu Bala kan yadda ya gyara kasuwar, ta hanyar yi mata gini irin na zamani.
“Muna rokon Karamar Hukumar ta zo ta bude wajen kasuwar da aka gyara, domin a halin yanzu ’yan kasuwar suna cikin kunci a wuraren da suke sayar da kaya, saboda cunkoso ya yi yawa a kasuwar, sakamakon rashin bude ta.’’