✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a 2022 

Hukumar ta bayyana dalilai da dama da suka haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufin.

Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ya haura zuwa kashi 23.72 cikin 100 a watan Oktoban bana, wanda ya yi daidai da kashi 5.39 bisa 100 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Oktoban bara da kashi 18.34 cikin 100 kamar yadda rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan ya karu zuwa kashi 21.09 cikin 100, wanda ya kasance mafi girma a shekara 17.

Hukumar ta bayyana cewa hauhawar farashin ya samo asali ne sakamakon tashin farashin burodi da hatsi da kayan abinci kamar dankali da dawa da sauransu.

A kididdigar wata-wata, hukumar ta ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Oktoba ya kai kashi 1.23 cikin 100, wanda shi ne mafi karanci da kashi 0.21 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Satumban 2022 (kashi 1.43).

Hukumar ta bayyana cewa an samu raguwar farashin wasu kayayyakin abinci kamar dabino, da masara, da wake, da kuma kayan ganyayyaki.

A halin da ake ciki, hukumar ta ce farashin kayayyaki ya kan karu a duk wata-wata, inda ya kai kashi 1.2 cikin 100 wanda ya yi kasa da kashi 0.11 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Satumban 2022 (kashi 1.36).

Sai dai hukumar ta ce a cikin watanni ukun da suka gabata, an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki saboda raguwar sauye-sauyen da aka samu a kididdigar abinci da lokacin girbi.

NBS ta kara da cewa, an samu karin kudin ne saboda janyewar kayan abinci, da karuwar farashin shigo da kayayyakin daga kasashen waje, sakamakon faduwar darajar kudin da kuma karuwar farashin kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.

Haka kuma, NBS ta alakanta lamarin da iftila’in ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu sassan Najeriya.