✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farashin gyada ya fadi warwas a Taraba

Farashin gyada ya sauka da fiye da rabi a kasuwanni.

Binciken Aminiya ya gano cewa girbin da manoman gyada suka yi ya yi sanadiyyar karyewar farashin gyada da fiye da rabi a Jihar Taraba.

A watannin da suka shude ana sayar babban bahun gyada mai nauyin kilogram 100 a kan N21,000, amma a yanzu ya koma tsakanin N7,000 zuwa N9,000.

Bincikenmu ya gano cewa manoma sun cika kasuwannin Maihula da Garba-Chede da gyada, a yayin da masu saye daga duk sassan Najeriya ke zuwa don sayen kayan yau da kullun.

Wani manomi a Maihula, Dauda Yusuf, ya shaida wa Aminiya cewa  girbin gyadan da suka yi ya yi musu rana a wannan shekarar.

Ya ce sabanin shekarar da ta gabata da amfanin da suka samu ya yi karanci saboda rashin isasshen ruwan sama, a bana an samu karin ruwan sama wanda ya kai ga samun gyada mai kyau.

Wani dillalin gyada daga Kano, Alhaji Nasiru Saidu, ya shaida wa Aminiya cewa a bara manoma ba su samu gyada ba sosai shi ya sa aka samu karancin gyada a jihar.

Ya ce da yawa daga cikin masu samar da man gyada suka koma sayen gyada daga kasuwar ta Maihula a matsayin babban tushen gyada.

Ya kara da cewa idan aka samu girbi mai yawa, za a sami isasshiyar gyada daga manomanta, kuma masu amfani da ita za su same ta a kan farashi mai rahusa a bana.