Rahoto Farashin Man Fetur a Duniya ya nuna cewa farashin man fetur na Najeriya a cikin gida shi ne na 22 a fadin duniya.
Rahoton da aka yi wa take da ‘Farashin Mai’ ya nuna cewa matsakaicin farashin fetur a duniya shi ne Dalar Amurka 1.30 a kowace lita.
- Yobe ta Gabas: Surikin Minista Gaidam Na Takarar Kujerarsa
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Kauce Wa Talauci A Watan Janairu
Matsakaicin farashin man fetur na Najeriya ya kai N660.25 ($0.722), musamman a shekarar da muke ciki, 2024.
Rahoton da aka fitar a watan nan na Janairu ya nuna cewa kasashe masu arziki sun fi tsadar fetur, a matalautan kasashen da ke samar da shi kuma akwai saukin farashi a cikin gida.
A cewar rahoton, kasashen da suka fi arhar fetur a duniya su ne; Iran, inda farashin lita ya kai N26.52 ($0.029), sai Libya N28.35 ($0.031) sannan Venuezela a kan N32.01 ($0.035) kowace lita.
Wurin da man fetur ya fi tsada a duniya shi ne Hong Kong, inda farsahin lita ya kai N2,835.77 (Dala $3.101) kowace lita.
Haka zalika man na da tsada a kasashen turai inda birnin Monaco farashin lita ya kai N2,151.75 ($2.353) sai Norway, N1,876.49 (2.0520.
Kazalika, Najeriya ce kasa ta 67 a jerin kasashe masu tsadar man dizal, yayin da Venezuela, Iran da Libya ke kan gaba wajen tsadar man dizal din.
Najeriya ce kasa mafi arzikin mai a Afirka a watan Nuwamban 2023 inda kasar ke hako ganta militan 1.25 a kullum.
Sai da a halin da ake ciki kasar na fama da karancin tataccensa a cikin gida, amma ana ran a bana za a samu sauki idan matatar man Dangote da wasu na gwamnati suka fara aiki.