Farashin gangar danyen mai ya yi tashin gwauron zabo zuwa kusan Dala 84 kowace ganga a ranar Talata.
Tashin farashin gangar man, samfurin Brent, shi ne kololuwar da aka samu a cikin shekara uku, a yayin da a halin yanzu aka samu karuwar bukatar albakartun man.
Hakan na farkuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin mai, musamman a manyan kasashe masu masana’antu irin China da sauransu, a yayin da kasashe ke farfadowa, harkokin tattalin arziki kuma na kara bunkasa.
Sai dai kungiyar kasashe masu arzikin mai da dangoginsu (OPEC+) ta ce mambobinta za su ci gaba da samar da mai a kasuwar duniya amma sai a hankali za su kara adadinsa da suke samarwa.
“OPEC+ za ta ci gaba da samar da adadin man yadda ta tsara har zuwa karshen shekara, saboda haka sai dai a lallaba,” inji wani jami’in kamfanin dillancin mai na PVM, Stephen Brennock.
– Brent ya yi tashin gwauron zabo
A ranar Talata, farashin danyen mai samfurin Brent ya kai Dala 83.67 kowace ganga bayan ya kai Dala 84.60 a ranar Litinin, wanda tun watan Oktoban 2018 rabon da a ga irin hakan.
“Ba abun mamaki ba ne idan a cikin makon nan aka samu karin Dala biyar zuwa Dala takwas a kan farshin kowace gangar mai,” a cewarsa.
Zuwa yanzu, farashin mai samfurin Brent ya karu da kashi 60 cikin 100 ke nan a shekarar da muke ciki.
– Tsugune ba ta kare ba
Hakan na da alaka da tsadar farashin iskar gas a kasashen Turai fiye da kowane lokaci, lamarin da ya tilasta komawa amfani da man fetur.
A ’yan makwannin nan, farashin wutar lantarki ya yi tashin gwauron zabo sakamkon karancin man fetur a kasashen Asiya da Turai da Amurka.
Ana kuma hasashen cewa karancin mai a kasar China za ta kai wa har uwa karshen shekarar da muke ciki.
A ranar Litinin, wani jami’in gwamnatin Amurka, ya ce Fadar White House na ci gaba da kira ga kasashe masu arzikin man fetur da su kara dagewa wajen hako shi domin domin ya wadata a kasuwar duniya.