✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin abinci ya karu a Gombe

Ganin cewa idan watan Azumi ya kama a kan samu sauyin farashin kayayyaki a kasuwanni musammam kayayyakin masarufi da na marmari, wakilinmu da ke Gombe,…

Ganin cewa idan watan Azumi ya kama a kan samu sauyin farashin kayayyaki a kasuwanni musammam kayayyakin masarufi da na marmari, wakilinmu da ke Gombe, ya ziyarci babbar kasuwar Doya da ta kayan marmari, inda ya jiyo mana yadda farashin kayayyakin suke a wannan wata.
A kasuwar Doya ya samu jin ta bakin wani mai sayar da doya mai suna Sale dan Zaki,  inda ya ce ba zuwan azumi ne ya kawo tsadar doya ba, karancinta ne domin yanzu haka ta fara karewa kuma sabuwa ba ta shigo ba.
Ya ce karamar doya da ake sayarwa Naira 500 zuwa 600 a yanzu, a baya ba ta wuce Naira 350 zuwa 400, har ta 550 akwai, amma yanzu sai fin haka wato 600, 700.
Kodayake, ya ce nan da wasu ’yan kwanaki kafin azumi ya kare ma za ta iya yin sauki saboda lokacin sabuwa za ta fara shigowa, amma duk da tsadar da take da shi a ba na tafi shekarar bara sauki saboda yanzun ba kudi ne a kasa shi ya sa ake ganin tsadar ta.
Shi ma wani mai sayar da dankalin Turawa mai suna Iliyasu Alhaji Idi, cewa ya yi farashin dankalin a yanzu haka ya danganta da irin kyawunsa da kuma yadda ya zo domin yanzu ana da bukatarsa ne kuma babu shi. Hakan ya sa ya yi tsada domin tsohon ya fara karewa sabon kuma bai wadata ba. Har ila yau, ya ce tsohon dankalin ya fi tsada amma duk da shi ma sabon yana da tsada, amma shi tsadarsa rashin wadatuwarsa ne amma ka ga yanzu sabon muna sayar da garwa guda Naira 2200 a baya kuma bai wuce 1500. Hakazalika, kwando yanzu Naira 1200 muke sayarwa, a baya kuma bai wuce 600 tsadarsa 800, ita ma robar shan ruwa Naira 600 ce mai maimakon naira 200 zuwa 300 a baya lokacin da yake a wadace.
A kasuwar kayan gwari kuwa ta Lemo da Ayaba da Kankana, Adamu Mai Lemo Yaron Yahaya cewa ya yi kayan gwarin sun yi wahala ne shi ya sa suka yi tsada, amma kafin zuwan azumi kayan sun fi sauki a kan yanzu.
Ya ce karamar ayaba a wajensu Naira 400 ce suke saya su kuma su sayar 600 ko 550 a hakan mutane na korafin cewa suna tsada kuma ba ta samuwa ne domin duk girman Jihar Gombe ba ta wuce mota daya ake samu kankana kuma 250 ita ce karamar wacce a baya ba ta wuce Naira 70. Hakazalika, ita ma abarba wacce suke sayarwa Naira 500 a yanzu ita suke sayarwa 200 zuwa 300 kafin zuwan azumi.
A kasuwar kayan miya ba a samu danyen kaya ba, kamar tattasai da tumaturi saboda sun yanke don sun yi tsada ba sa samuwa. Busashe kuma ya yi tashin gwauron zabi daga Naira 250 zuwa 400 wani wurin  300. Tamanin tumaturi kuma Naira 250 maimako 150 a baya.