✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Faransa za ta taimaka wa Najeriya yaki da fashin teku

Faransa ta ce za ta hada kai da Najeriya wajen yakar masu fashin gabar tekun Guinea.

Gwamnatin Faransa ta bayyana aniyar taimakon Najeriya wajen yaki da fashin teku a gabar ruwan kasar Guinea wanda aka  dauki tsawon lokaci ana fama.

Hakan ya fito ne daga bakin Babban jami’in Tsaron Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya, Kanar Nicolas Rambaud, a ranar Laraba yayin ziyarsa a Cibiyar Horar da Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Fatakwal.

Rambaud, ya ce “Muna sane da irin halin barazana da Najeriya ke fuskanta daga gabar ruwan Guinea.

“Za mu taimaki Najeriya wajen fito da sabbin tsare-tsare na horo ga sojin ruwa, don magance fashin jirage da garkuwa da mutane”.

Ya kara da cewa, Faransa na da muradai da dama wajen bunkasa alakarta da Najeriya, kuma wannan dama ce da za su nuna hakan a zahiri.

Jami’in ya ce sun gamsu da rawar da sojin ruwan Najeriya ke takawa kuma ta hanyar hadin kan da ke tsakanin kasashen, za a iya samun ci gaba.

Kanar Rambaud ya kuma yaba wa Najeriya saboda sayen jiragen yakin ruwa guda 17 daga kamfanonin Faransa a cikin shekarun da suka gabata.

Kazalika, ya sanar da cewa a cikin makonni masu zuwa Najeriya za ta karbi wani katafaren jirgin ruwan da ke dauke da na’urorin zamani daga Faransa.

Jirgin ruwan da ake wa lakabi da NNS Lana, yana dauke da ingantattun na’urorin zamani kuma zai bar Faransa ne a ranar 16 ga watan Afrilu zuwa Najeriya.

Kwamandan da ke kula da makarantar sojin ruwan Najeriya, Kaftin Mahmud Fana ya bayyana makarantar tasu a matsayin guda daya tilo a yankin Afirka ta Yamma.