✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Faransa ta sake kiran Benzema a karon farko bayan shekara 6

Faransa ta dawo da dan wasan bayan shafe shekara shida baya taka mata leda.

Mai horar da ’ya wasan kwallon kafar kasar Faransa, Didier Dechamps, ya gayyaci dan wasan gaban Real Madrid, Karim Benzama domin taka leda a gasar cin kofin EURO da za a yi a watan Yuni.

Tun a shekarar 2015, Faransa ta dakatar da Benzema daga buga mata wasanni.

Dakatarwar da aka yi dan wasan na da nasaba da zargin sa da hannu a bidiyon fyade da dan wasan kasar Valbuena ya yi.

Dechamps ya ce akwai matakai daban-daban da aka bi kafin gayyatar Benzema, kuma shi da dan sun riga sun tattauna.

Benzema da ya jefa wa Faransa kwallaye 27 a wasanni 81 da ya buga mata.

A bana, Benzema ya jefa wa Real Madrid kwallaye 29, adadin da ya zarce kwallaye 20 da ya saba jefawa kowace shekara tun bayan barin Cristiano Ronaldo Real Madrid zuwa Juventus a 2018.

Bajintar da dan wasan ya nuna, ta sa Faransa ta sake kiran sa don ci gaba da murza mata leda.

Tuni dai Benzema ya wallafa sakon murna da godiya ga ’yan uwansa, abokai da wanda suka dage wajen ganin sake kiran nasa.