✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa ta kori ’yan Rasha 6 kan zargin leken asiri

Ana zarginsu da fakewa da aikin karfafa alakar huldar diflomasiyya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta yanke shawarar korar wasu ’yan kasar Rasha 6 da ake zargi da yin leken asiri, ta hanyar fakewa da aikin karfafa alakar huldar diflomasiyya.

Matakin Faransa na korar ’yan kasar ta Rasha ya biyo bayan binciken da jami’an leken asirin Faransa suka gudanar wanda ya bankado shirin sirri da jami’an diflomasiyar ke aiwatarwa.

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan nau’in ayyuka ko leken asirin da ake tuhumar jami’an diflomasiyyar na Rasha da aikatawa ba.

A ranar 4 ga watan Afrilu Faransa ta ce za ta kori jami’an diflomasiyyar Rasha 35, a wani mataki na hadin gwiwa da kasashen Turai suka dauka bayan yakin da shugaba Vladimir Putin ya ba da umarnin kaddamarwa kan Ukraine a karshen watan Fabarairu.

Kasashen Turai da dama dai sun kori jami’an diflomasiyyar Rasha, musamman bayan bankado makeken kabarin da aka yi dauke da gawarwakin fararen hula kusan 300 a garin Bucha da ke kusa da Kyiv babban birnin kasar Ukraine.