Ministan Watsa Labarai da A’ladu Alhaji Lai Mohammed ya ce kasar Faransa ce hedkwatar da aka tara kudin gudanar da ayyukan kungiyar Neman kasar Biyafara (IPOB).
Minista Lai Mohammed, ya bayyana haka ne ga manema labarai na fadar Shugaban kasa da ke Abuja a shekaranjiya Laraba, bayan kammala taron Majalisar Zartarwa, inda ya ce, shaidu sun nunamasu neman ballewar suna samun kudi daga nan cikin gida da kuma kasashen waje kuma Gwamnatin Tarayya ta san inda kudaden suke fitowa.
Ya ce: “Muna da shaidu, mun san kungiyar IPOB tana karbar kudi daga mutane da dama a kasashen waje da kuma mutane da dama a nan Najeriya, kuma suna karbar kudi daga wasu kasashen waje, wannan a fili yake. Kuma ina shaida muku cewa hedkwatar tattara kudin tana Faransa ce, mun sani… kuma wajibi ne ka toshi hanyoyin samar da kudaden wannan shi ne abin da na fadi kwanakin baya.”
Ya kara da cewa: “Abu ne da ya tabbata wadansu mutane da suke kasashen waje suna bayar da kudi ga IPOB, inda take samun kudinsa ke nan. Mun san wannan kuma a magana ta gaskiya akwai wasu batutuwa na diplomasiyya masu sarkakiya da ke bukatar ka tsallake su.”
Da aka nemi ya fadi masu bai wa IPOB kudaden, sai Ministan ya ce: “Ina jin ba wani abu ne da za a tsaya dogon nazari ba. Duk wanda ya saci kudin gwamnati zai yi duk mai yiwuwa domin daga hankalin gwamnati. Abin Allah Ya kiyaye idan kasar nan ta auka cikin yaki… Me gwamnati za ta fi mayar da hankali a kai? Shi ne kokarin magance tashin hankali. Don haka wata hanya ce ta karkatar da hankali a tabbatar an rikita gwamnati ta rasa makama. Ba na son jawo takaddamar diplomasiyya, muna da hujja kan inda kudaden suke zuwa… kuma muna aiki a kan haka ba za mu dakata ba.”
Ingila ta ki rufe rediyon Biyafara Ministan ya kuma nuna damuwa kan duk da yadda gidan rediyon Biyafara ke jawo barna a Najeriya, amma kasar Birtaniya ta ci gaba da barinsa yana aiki a kasarta ta hanyar fakewa da ’yancin fadin albarkacin baki.
Ya ce: “Da za a samu wani mutum a Najeriya ya fito fili yana neman makamai don ya je ya yaki Ingila, me za ku yi tunani a kai? Shin za ku dauki hakan a matsayin ’yancin bayyana ra’ayi? Wannan fa kasa ce da take da wani tarihi; me Iraki ta yi aka jingina mata ta’addanci?”
Da aka tambaye shi ko Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da a haramta kungiyar IPOB, sai ya ce: “Akwai hanyar haramtawar; kuma Babban Lauyan Tarayya zai bi hanyar kuma yana yi. Amma shin za ku so Shugaban kasa ya jira sai an kafa doka kafin ya dauki matakin hana kwasar dukiyar jama’a da kashe-kashe? Yaya Najeriya za ta kasance a yau in da an samu daukar fansa a Legas da Kano? Kamar yadda Gwamnan Abiya ya fadi jiya (ranar Talata), akwai kimanin Ibo miliyan 11 da suke zaune a wajen Kudu maso Gabas; wannan adadi ne mai yawa ba abin wasa ba ne.”
Ministan ya ce, an ci sa’a sosai a makon jiya “da an samu gagarumin zubar da jini in da an dauki fansa a wajen Kudu maso Gabas.” Ya ce an kauce wa haka ne saboda sarakuna da gwamnonin jihohi da sauran shugabanni sun ‘rika tausar mutane.’
A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ’yan ta’adda, bayan da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta amince da bukatar haka da gwamnatin ta kai mata.
A makon jiya Rundunar Sojin kasar nan ta yi irin wannan shela, amma daga bisani ta janye bayan da wadansu suka yi ta sukar ba ta da hurumin yin hakan kai-tsaye.
kungiyar IPOB ta ce ita ba kungiyar ’yan ta’adda ba ce.
Gwamnatin ta ce ta samu izinin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, lokacin da ta kai batun ga kotun cikin gaggawa domin samun sahalewar kotun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan takardar haramta kungiyar.
Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Malam Abubakar Malami, ya tabbatar wa gidan rediyon BBC cewa izinin kotun ya ba su damar ayyana kungiyar a matsayin ta ’yan ta’adda.