✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FAO ta ciri tuta a Arewa maso Gabas

Tallafin Hukumar Noma da Abinci ta duniya ‘Food and Agriculture Organization (FAO) ya kai ga magidanta dubu 138 da 801 daga cikin magidanta dubu 141…

Tallafin Hukumar Noma da Abinci ta duniya ‘Food and Agriculture Organization (FAO) ya kai ga magidanta dubu 138 da 801 daga cikin magidanta dubu 141 wadanda ta yi hasashen tallafawa a lokacin rani a bana. Wannan adadi ne kuma ya hada daidaikun tallafin ya kai dubu 971 da 607 a jihohin Borno da Adamawa da Yobe baki daya.

Jakadan hukumar FAO na Najeriya, Patrick Dabid ne ya bayyana haka a yayin taron wata-wata na PCNI a wannan wata. Tare da hadin gwiwar cibiyoyi daban-daban, FAO ta samu damar raba itatuwan dashe, magungunan feshi da kuma irin shuka a matsayin gudumawarta ga kyautata zamantakewa ga dubban al’ummomin Arewa maso Gabas. Sakamakon ya nuna cewa kimanin kashi 25 cikin 100 na wadanda suka amfana da shirin mata ne. Sannan wadanda aka dawo da su, ‘yan gudun hijira da kuma sauran kauyukan sun kai kimanin kashi 41, yayin da kashi 38 suka amfana daga sauran sassan.

Jakadan hukumar a Najeriyar ya koka game da wasu matsaloli da suka hada da rashin isasshen zaman lafiyar da ke barazana bisa komawar wasu gonakinsu a yankin da noman ke da matukar tasiri. Haka kuma ya yi hasashen yiwuwar ambaliya a Yobe, rashin isar tallafin zuwa wasu wuraren. 

Amma a shirinta na tunkarar badi, FAO tare da hadin gwiwar Jihar Borno sun lashi takobin kyautata al’amuran samar da isassun kayayyakin noma fiye da bana, wadanda suka hada da injunan ban ruwa da sauransu, wadanda za su isa ga kimanin magidanta dubu 97 da 750.