Uwargidan Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, Ummi, ta nuna damuwarta kan fannin ilimin Najeriya, inda ta ce ya tabarbare matuka.
Ummi El-Rufai ta yi wannan bayani ne a wajen kaddamar da makarantar zamani wadda Fifth Chukker tare da hadin gwiwar Bankin Access suka gina a Maraban Jos, Jihar Kaduna.
- Tinubu ya bai wa mutanen da aka kai wa hari a coci tallafin N75m
- Mayakan Boko Haram sun tare hanyar Damaturu-Maiduguri
Hajiya Ummi, wadda Jakadiya ce ta UNICEF, ta ce “…Fannin ilimin Najeriya ya tabarbare, hatta damar da kananan yara za su yi karatu babu ita.
“Don haka irin wannan aiki abu ne da kowa zai so a yi da shi kuma ina matukar alfaharin ni ma aikin ya shafe ni.”
Uwargidan gwamnan ta ce, iyayensu kyauta suka samu ilimi kuma mai inganci a shekarun baya sabanin zamanin yau.
Daga nan ta yaba wa Fifth Chukker da Bankin Access dangane da samar da makarantar don amfanin al’ummar yankin da lamarin ya shafa.
Makarantar dai ana sa ran za ta dauki daliban da yawansu ya kai 12,000.
Ta kara da cewa, idan ana samu irin wadannan makarantu a karkara, iyaye ba za su matsa wa kansu tura ’ya’yansu makarantun kudi ba saboda za su samu ilimi mai nagarta.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, mu’assasin Fifth Chukker, Adamu Attah, ya ce a shekarun da suka gabata shi da abokan huldarsa suka nuna damuwarsu kan matsayin ilimi a Arewacin Najeriya wanda hakan ya sa suka dauki Makarantar Firamare ta Maraban Jos mai dalibai kasa da 500 sannan suka bunkasa ta ta yadda za ta iya daukar dalibai 12,000.