Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio, ya zargi ’Yan Majalisar Tarayya da karbar kwangila daga hukumar kula da yankin (NDDC).
Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana domin amsa tambayoyi a gaban Kwamitin kula da yankin na Majalisar Wakilai, a ranar Litinin.
“Mun bayar da kwangiloli ga ’yan majalisa. Ba lallai ne ki sani ba”, inji shi a lokacin da yake amsa tambayar daya daga cikin ‘yan kwamitin, Boma Goodhead, game da zargin hakan.
A baya kwamitin riko na NDDC ya zargi shugaban kwamitin, Olubunmi Tunji-Ojo, da karbar kwangiloli daga hukumar amma ya karyata.
A ranar Litinin Olubunmi Tunji-Ojo ya sauka daga mukaminsa, yayin da kwamitin ke ci gaba da sauraron bayanai kan zargin badakalar Naira biliyan 81.5 a NDDC.
Kwamitin rikon NDDC karkashin Farfesa Kemebradikumo Pondei ya bukace shi ya ajiye mukaminsa, a lokacin da shi da Akpabio suka bayyana a gaban Kwamitin wanda ya ba su wa’adin ranar Litinin din domin amsa tambayoyi.