Ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ta sanar cewa mutane 104 ne suka mutu, wasu fiye da 750 suka jikkata bayan sojojin Isra’ila sun bude wuta kan fararen hula da suka taru a wurin karbar kayan agajin yankin Falasdinu.
Kakakin ma’aikatar, Ashraf al-Qudra, ya ce adadin wadanda suka mutu sakamakon “kisan gillan” na ranar Alhamis a birnin Gaza ya haura zuwa shahidai 104 da kuma jikkata 760 sakamakon harbin da sojojin Isra’ila suka yi wa taron jama’an a yankin Nabulsi.
Majiyoyin Isra’ila sun tabbatar da harbin, tare da cewa sojojin sun bude wuta ne bayan da suka yi zargin barazana daga taron jama’a da ke kusa da wurin karbar kayan agajin.
Ma’aikatar ta ce zuwa adadin mutanen Isra’ila ta kashe a Gaza ya zarce 30,000 daga lokacin da Isra’ila ta fara kai hari a yankin a watan Oktoban 2023 zuwa yanzu.
- ’Yan bindiga sun sace mutane 30 a Sallar Asuba a Zamfara
- Tsadar rayuwa: Nama ya gagara, an koma cin awara
Kwararru dai na ganin adadin ba shi ne hakikanin alkaluman wadandana aka kashe ba, lura da yadda ake wahalar samun bayanan mace-mace a yanayin yaki da kuma katsewar sadarwa da rugujewar tsarin kiwon lafiya a Gaza.