Mahukuntan Isra’ila sun ce Falasdinawa sun lalata wani wuri mai tsarki na Yahudawa a Nablus, a yayin da rikici ke kara kamari tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra’ila a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Wani shafin Twitter na gwamnatin Isra’ila ya wallafa wani bidiyo da ya ce ke nuna yadda Falasdinawa ke kai hari a wurin da Yahudawa ke ganin ya kunshi kabarin Annabi Yusuf.
- Dalilin da muke son kwato Kano daga APC da PDP — Dokta Isyaku Rabi’u
- PRP za ta iya samar da wanda zai gaji Buhari — Falalu Bello
Zuwa yanzu babu wani martani daga bangarorin Falasdinawan kamar yadda BBC ya ruwaito.
Yahudawa na girmama wurin da kabarin yake, amma yana cikin yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
An sha yin arangama a wurin, har ta kai aka kona kafin aka sake gyarawa.
Ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz ya bayyana al’amarin a matsayin “babban laifin saba ’yancin ibadah”.
Yankin Yamma da Kogin Jordan na fuskantar barazanar tsaro tun bayan farmakin da sojojin Isra’ila suka kaddamar bayan harin da aka kai a Tel Aviv da kuma cikin yankin Isra’ila.