Falasdinawa shida sun gudu daga inda ake tsare da su a gidan kurkukun kasar Isra’ila ranar Lahadi, kamar yadda sojojin kasar suka tabbatar a shafinsu na Twitter ranar Litinin.
Yanzu haka dai sojojin kasar tare da gudunmawar ma’aikatan liken asirin kasar da ma jami’an ’yan sanda sun dukufa nemo fursunonin.
Sun dai tsere ne ta wani rami daga gidan kurkukun Gilboa mai tsananin tsaro da ke Arewacin kasar, inji hukumar gidan yarin kasar.
A cewar rahotanni, fursunonin Falasdinawan sun haka rami ne da ya hadu da wani haka da wasu mutane suka yi daga waje a dab da gidan yarin.
An dai daure akasarinsu ne bisa zargin kai hari kan Yahudawan Isra’ila, inji kafafen yada labaran kasar.
Daruruwan ragowar fursunoni ne dai yanzu za a kwashe domin canza musu gidajen yari a matsayin shirin ko-ta-kwana.
Kungiyar Falasdinawa masu tayar da kayar baya da ke Zirin Gaza ta bayyana guduwar a matsayin wani mataki na jarumta, inda ta ce hakan ba karamin cin fuska ba ne ga gwamnati da sojojin Isra’ila. (NAN)