Shugaban jam’iyyar SDP, Cif Olu Falae ya yi kira da a sami hadin kai don a cire Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019.
Falea wanda ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a garin Abekuta jiya ya ce kamar yadda kowa ya sani ne abubuwa ba sa tafiya kamar yadda ya kamata sabanin alkawarin da jam’iyyar APC ta yi a shekarar 2015.
Ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ya je garin Abekuta ne don ya nemi goyon bayan takararsa ta shugaban kasa.
Ya bayyana cewa halin da kasar ta shiga ya fi Karin burin tsayawa takarar ta wani dan siyasa a kasar.
“Na zo nan ne don na yi musayar ra’ayi da Baba Obasanjo kan al’amuran Najeriya. Akwai lokacin da a tsakanin shekarar 1977 da 1979 na yi aiki da shi lokacin da yake shugaban mulkin sojan Najeriya ni kuma ina matsayin sakataren dindin. Mun yi abubuwa masu yawa a wannan lokaci don ci gaban Najeriya. Yadda abubuwa ke tafiya a yanzu saboda haka ina bukatar na yi musayar ra’ayi da shi kan ci gaban Najeriya”. Inji shi