✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fa’idoji 6 da ’yan Najeriya za su samu daga bututun iskar gas na AKK

Ranar Talatar makon jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin shimfida bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano ta Kaduna (AKK). Idan aka…

Ranar Talatar makon jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin shimfida bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano ta Kaduna (AKK).

Idan aka kammala aikin shimfida bututun na AKK dai zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ta muhimman hanyoyi shida kanar haka:

1. Samar da ingantacciyar wutar lantarki

Iskar gas din da za a kwararo ta wadannan bututai za ta taimaka wajen samar da megawatt 3,600 na wutar lantarki.

2. Samar da ayyukan yi, musamman ga matasa

Aikin zai samar da ayyukan yi masu yawa, musamman ga matasa.

An ambato shugaban daya daga cikin kamfanonin da za su yi aikin wato Oilserv Limited, Injiniya Emeka Okwuosa, ya ce kamfanin nasu zai debi ma’aikata 3.000.

3. Bunkasa kwarewa da fahimtar mutane kan wata sabuwar fasaha a wuraren da bututun zai ratsa

Ana fata ’yan Najeriya a yankunan da aikin ya ratsa za su koya sabbin dabaru ko fasahohin aiki’ sannan wadanda ke aiki wajen shimfida bututan za su samu Karin kwarewa.

4. Samar da makamashi ga dimbin masana’antun da suka durkushe, musamman a Arewacin Najeriya

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa a Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya kiyasta cewa yawan iskar din da za a samar zai kai gangar mai sama da miliyan 391.

Ana sa ran wannan zai taimaka wajen farfado da masana’antun da suka durkushe saboda karanci ko rashin makamashi, musamman a arewacin Najeriya.

5. Samar da kudin shiga ga kasa

Najeriya ce kasa ta bakwai a yawan albarkatun iskar gas, amma ta fi mayar da hankali wajen hako man fetur duk da iskar gas ta fi kawo kudin shiga – don haka aikin zai kara yawan kudin shigar da kasar ke samu.

Sai dai kuma kamfanoni masu zaman kansu ne za su samar da kudin aikin, kuma za su fanshe abin da suka kashe kafin ya zama mallakin gwamnati.

6. Bunkasa tattalin arziki a jihohin da bututun ya ratsa

A cewar Shugaba Buhari, aikin zai habaka cigaba ya kuma inganta masana’antun yankunan da ya shafa a jihohin Kogi da Neja da Kaduna da Kano da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.