✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fafaroma ya nada mace ta farko ta jagoranci majalisar fadar Vatica

Ita ce dai za ta kasance macen da ta rike mukamin na biyu mafi girma a fadar.

A karon farko a tarihin fadar Vatica, Fafaroma Francis ya nada mace ta rike wani matsayi a majalisar fadar.

Raffaella Petrini ita ce dai aka ayyana sunanta a matsayin sabuwar Babbar Magatakardar Majalisar Fadar ta Vatica, kamar yadda aka sanar a ranar Alhamis.

Ita ce dai za ta kasance macen da ta rike mukamin na biyu mafi girma a fadar.

Za dai ta kula da gidajen tarihi na fadar da sauran muhimman wurare da kayayyakinta.

Kafin nadin nata, Raffaella, mai kimanin shekara 52, ita ce take kula da babban sashen da ke kula da wa’azi da yada addinin Kiristanci a fadar.

A ’yan watannin da suka gabata dai, masharhanta na ganin cewa Fafaroman ya mayar da hankali sosai wajen la’akari da mata a mafi yawan nade-naden da yake yi.

Ko a farkon shekarar nan sai da ya nada Nathalie Becquart a matsayin mace ta farko a tarihin Cocin Katolika da za ta yi aiki a matsayin Sakatariya a majalisar limaman cocin.

Bugu da kari, a watan Agustan da ya gabata ma, Fafaroman ya bayyana sunan Alessandra Smerilli a matsayin Sakatariyar riko a Hukumar Ci Gaban Al’umma ta fadar.

Hukumar dai ta fi mayar da hankali ne wajen tallafa wa ’yan gudun hijira da yaki da talauci. (NAN)