Wata motar tanka da ke dauke da man fetur ta fadi a mahadar hanya ta Dikko da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, da ke jihar Neja.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 8 da rabi na daren Juma’a ya haddasa mutuwar mutum 5 da kuma jikkata sama da 10 kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Wasu da su ka zanta da wakikinmu a wajen a yau Asabar , sun bayyana cewa direban tankar ya fito ne daga bangaren Zuba inda ya yanke shawarar tsaida motar a wata tashar gefen titi da ke wajen bayan an wuce gadar sama.
Sun yi bayanin cewa duk yunkurin dakatar da direban daga bangaren masu lodin fasinja a wajen da kuma masu shagunan baca bai samu nasara ba, kuma nan take bayan motar ya rabe daga gabanta inda man da ta ke dauke da shi ya kwaranye bayan faduwar bayan motar.
Motoci sama da 19 ne su ka kone a sakamakon gobarar da ta biyo bayan faduwarta, sai kuma shagunan baca 35.
Sakataren gwamnatin jihar malam Ahmed Ibrahim Metene wanda ya kai ziyarar jaje a yau a madadin gwamnan jihar Muhammad Sani Bello wanda ke kasar waje kamar yadda ya yi bayani, ya ce gwamnatin jihar zata kawar da tashar wucin gadi da ke gefen titin da kuma sauran masu sana’a.
Sakataren wanda ya sami rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar wanda kuma shi ne ke wakiltar karamar hukumar Tafa a majalisar, yankin da lamarin ya faru, ya ce muhimmancin ran dan adam ya dara na duk wata sana’a, a saboda haka ya shawarci masu sana’o’i a wajen da su bar wajen tun gabanin aikin kawar da su din, inji shi.