✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar shugaban kasa ta soke shirin kafa Ruga

Fadar shugaban kasar Najeriya a yau Laraba ta tabbatar da soke shirin kafa rugage, an fara yunkurin kafa rugar ne don kawo karshen rikicin da…

Fadar shugaban kasar Najeriya a yau Laraba ta tabbatar da soke shirin kafa rugage, an fara yunkurin kafa rugar ne don kawo karshen rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a duk fafin kasar. Da nufin killace dabbobin makiyaya.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan.

Majiyar mu ta samu rahoton cewa, wasu Gwamnoni hudu a yanzu haka na ganawa da Mataimakoin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, akan batun shirin kafa ruga a jihohinsu.

Garba Shehu, ya ce bayan kammala ganawar da Gwamnonin ke yi da Mataimakin shugaban Najeriya za su sanar da halin da ake ciki game da shirin kafa ruga a jihohin na su.