✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Shugaban Kasa ta koka bisa kisan dabbobinta

Namun dajin sun hada da birai da beraye da manyan macizai da jemagu da nau’ikan tsuntsaye iri-iri, wadanda an kebe musu wurarensu.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana damuwarta bisa kisan da ake wa namun dajin da ke cikin gandun dajinta a baya-bayan nan.

Mahukunta Fadar Aso Rock, sun bayyana hakan ne ta bakin Sakataren Gidan Gwamnati, Tijjani Umar, a yayin da yake karbar tawagar masu kula da Gandun Daji Na Kasa tare da takwarorinsu a Fadar Shugaban Kasa, wadanda aka fi sani da ‘Royal Rangers’.

Umar, wanda ya jaddada mahimmancin kariya da kiyaye tsirrai da dabbobi a muhallansu na asali, ya kuma yi alkawarin inganta yanayin kiyaye muhalli ta hanyar daukar matakan da suka dace na kiyaye namun daji.

Bugu da kari, ya ce za a dauki matakan da suka dace domin kare yanayi da kuma mayar da nau’ikan namun daji da tsirrai da aka yi asararsu a fadar gwamnati.

Ya sanar da cewa, an kebe wasu wurare a Fadar Shugaban Kasa domin zama muhalli ga wasu nau’ikan namun daji.

Namun dajin a cewarsa sun hada da biran tantalus da kadoji da katon kunkuru da manyan macizai da berayen daji da zabbi da jemagu da nau’ikan tsuntsaye iri-iri, wadanda an kebe musu wurarensu.

Ya kuma yi kira ga ma’aikata da masu ziyarar fadar da su guji cutar da halittun, inda ya kara da cewa za a kafa alamomi a wasu wurare domin wayar da kan jama’a kan bin ka’idojin da suka dace.

Umar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ta hannun Daraktan Yada Labarai, Abiodun Oladunjoye, ya taya Royal Rangers da sauran takwarorinsu na Najeriya murnar zagayowar Ranar Masu Kula da Gandun Daji ta Duniya ta bana, wanda aka yi a ranar 31 ga watan Yuli.