A karon farko Fadar Shugaban Kasa ta yi magana game da dakatar da Ibrahim Magu daga shugabantar hukumar yaki da almundahana ta EFCC, biyo bayan zarginsa da badakala.
A sakon da kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya wallafa a Twitter, Fadar Shugaban Kasar ta ce dakatarwar ita ce mafi a’ala, la’akari da irin zargin da shugaban hukumar yake fuskanta.
“Akwai zarge-zarge da yawa a kan mukaddashin shugaban EFCC da wasu ma’aikatansa, kuma da aka duba sai aka ga akwai bukatar yin da cikikakken bincike wanda ya haifar da kafa kwamitin binciken kamar yadda doka ta yi tanadi”, inji Garba Shehu.
A ranar Alhamis 9 ga watan Yuli ne Ministan Shari’a Abubakar Malami ya sanar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Magu tare da nada Umar Mohammed a matsayin mukaddashin shugaban EFCC zuwa lokacin da kwamitin zai kammala aikinsa.
Jami’in ya ce masu ganin binciken zai goga wa gwamnatin mai ikirarin yaki da rashawa kashin kaji, sun yi gurguwar fahimta domin abin da ta yi ya tabbatar da cewa ba ta da dan lele a yakin da take yi da zamba.
“Abin da ya kamata idan shugaban wata hukuma na fuskantar zargi irin wannan, shi ne ya koma gefe domin a samu yin bincike a kuma yi komai a fili ba tare da wani tarnaki ba”.
Ya kuma ce EFCC ba ta batun mutum daya ba ce don haka dakatar da mukaddashin shugaban nata zai ba da damar ta ci gaba da gudanar da harkokinta ba tare da wani tsaiko ba.
Magu ba shi da wata kariyar da za ta hana a bincike shi, kuma wannan dama ce gare shi ya kare kansa daga zarge-zargen, kamar yadda ya ce.
“EFCC na da hazikan ma’aikata da ke aikin ganin wasu tsiraru basu yi ruf da ciki kan dukiyar kasarmu ba, don haka su ma wajibi ne su fuskanci hukunci idan aka zarge su.