Fadar Buckingham ta kasar Birtaniya ta fara zaman makoki a ranar Juma’a bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth II, wadda ta shekara 73 a kan karagar mulki.
Sarki Charles III ne ya ayyana zaman makokin ga iyalan gidan sarautar, har sai bayan kwana bakwai da kai mahaifiyar tasa makwancinta.
- Yadda Jana’izar Sarauniya Elizabeth Za Ta Gudana
- Ana zargin shugaban makaranta da yin lalata da dalibansa 7 a Kwara
- DSS ta tsare mahaifin matar Tukur Mamu
Sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce, “Sakamakon Rasuwar Sarauniya Mai Daraja, Mai Alfarma Sarki yana fata za a fara zaman makoki daga yanzu zuwa kwana bakwai bayan jana’izar.
“Nan gaba za a sanar da bayanan gudanar da jana’izar” mahaifiyar tasa.
Baya ga iyalan gidan sarautar, ma’aikata da jami’an tsaron fadar za su bi sahu a lokacin makokin.
A tsawon lokacin, za a saukar da tuta kasa-kasa a gidajen sarautar har zuwa washegarin jana’izar.
Za a yin harbin bindiga 96, daidai yawan shekarun marigayiywar a duniya, a ranar Juma’a da misalin karfe 1 na rana agogoin GMT a dandalin Hyde Park da ginin Tower of London.
Za kuma a rufe gidajen sarautar har zuwa bayan jana’izar.
Jami’an fada sun shawarci masu son ajiye furanni a Fadar Buckingham da su yi hakan a wani wuri da aka ware a dandalin Green Park da kuma Hyde Park.
Za kuma a bude littafin karbar ta’aziyya a shafin masarutar ta intanet kuma, gwamnatin kasar Birtaniya za ta bayar da sanarwar gudanar da jana’izar.