✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fada a jirgi: Okorocha bai ga komai ba tukuna —Basarake

Ya ce Okorocha ya kwana da shirin sabon fada, idan suka sake gamuwa

Basaraken da suka ba hamata iska da tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya ce, Eze Cletus Ikechukwu Ilomuanya, ya ce Okorocha ya guji haduwarsu na biyu domin har yanzu da sauran rina a kaba.

Aminiya ta kawo rahoton yadda aka dambace tsakanin Okorcha da basaraken, inda ya kwakkwada wa tsohon gwamnan sanda, a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Owerri, Imo babban birnin Jihar Imo.

“Kwatar sa da aka yi da kyar bayan luguden naushin da basaraken ya yi mishi a cikin jirgin Air Peace somin tabi ne,” inji wata sanarwar da ya fitar.

A lokacin shugabancin Okorocha a Jihar Imo ne ya tube Eze Cletus daga sarautarsa da mukamin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Imo, ya kuma ki mayar da shi kan kujerar, duk da umarnin kotu.

Labarin fadar shugabannin biyu ya karade kafafen sada zumunta, amma daga baya wata kafar intanet ta ruwaito cewa basaraken ya musanta yin sa-in-sa da Okorocha a cikin jirgi.

Amma wata sanarawa da Eze Cletus, ya fitar da hannun kakakinsa, Kennedy Eweam, ya karyata labarin kafar intanet din.

Eze Cletus ya ce har yanzu bai yafe wa Okorocha ba, kuma ya kwana da shirin wani sabon karon batta, duk lokacin da suka sake gamuwa.

Sanarwar ta ce, ba don Allah Ya kiyaye ba, da basaraken ya lugwigwita Okorocha fiye da yadda ya yi masa.

“Bincikenmu ya gano cewa tsohon gwamnan ne ya dauki hayar kafar intanet din domin karyata labarin irin wulakancin da aka yi masa.

“Muna takaicin irin sakarci da wadancan ’yan jarida suka yi. Okorocha ya riga ya ja wa kansa bakin jini, ta yadda ba yadda ba abin da zai yi a ga farinsa.

“Okorocha ya tuna cewa kaikayi komawa take yi kan mashekiya.

“Akwai ma wasu ’yan Jihar Imo da ke jiran ranar da Allah zai hada su da Okorocha a kan hanya,” inji sanarwar.