An gurfanar da matar aure a Kotun Shari’ar Musulunci da ke cikin Hukumar Hisbah a Jihar Kano bisa zarginta da laifin lakada wa faccalarta duka.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ASP Habu Muhammad, ya shaida wa kotun cewa wata mata mai suna Zainab Muhammad Sheka ce ta yi karar matar dan uwan mijin nata mai suna Maryam Dauda a gaban kotun.
- Kotun Amurka ta samu Trump da laifin tayar da rikicin zabe
- Tuna Baya: Tarihin Janar Ibrahim Babangida
Maryam ta yi zargin cewa Zainab ta yi mata duka da itace ta yi ta kwada mata shi a goshi lamarin da ya janyo samun rauni a goshinta.
Takardar karar ta kara da cewa wacce ake zargin ta doki mai karar ne sakamakon zargin da ta yi mata cewa ta watsa mata shara a kofar dakinta.
Sai dai wacce ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da aikatawa na cin mutunci da gwada karfi da jin rauni.
Alkalin kotun, Mai Sharia Sani Tanimu Hausawa ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Agusta domin yanke hukunci.