✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FA ta ci tarar Liverpool da Everton

FA ta ce Liverpool da Everton na da daga yanzu zuwa ranar 20 ga watan nan don mayar da martani.

Hukumar FA ta ci tarar kungiyoyin kwallon kafa na Liverpool da Everton dangane da hatsaniyar da ta faru tsakaninsu yayin wasan hamayya da suka doka da juna a Litinin din da ta gabata.

Wasan wanda Liverpool ta yi nasara da kwallaye 2 da nema, FA ta samu bangarorin biyu da rashin da’a.

A cewar FA, kungiyoyin biyu sun gaza ladabtar da magoya bayansu kan yadda za su kauce wa irin hatsaniyar wadda ba ita ce karon farko da suka taba fuskanta.

Ana minti na 86 da wasa ne lokacin da Liverpool ke jagoranci da kwallaye biyun ne rikicin ya faro tsakanin Andrew Robertson da mai tsaron ragar Everton Jordan Pickford, ‘yan wasa biyu da tun a lokacin aka basu katin gargadi.

FA ta ce ‘yan wasan kungiyoyin biyu, hatta wadanda ke benci sun shiga hatsaniyar dalilin da ya sanya dukkanin kungiyoyin biyu za su fuskanci hukunci.

Hukumar ta FA ta ce Liverpool da Everton na da daga yanzu zuwa ranar 20 ga watan nan don mayar da martani kan hukunci tare da bayar da bahasin abin da ya faru.