Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta fara gudanar da bincike a kan yadda magoya bayan Ingila suka karya matakan tsaro a wasan karshe na gasar Euro 2020 da aka buga a filin wasa na Wembley, ranar Lahadi.
Wasu daga cikin magoya bayan na Ingila, sun yi kokarin kutsawa cikin filin wasan duk da rashin tikitin shiga .
- Za a fara daure barayin akwatin zabe shekara 20
- An kashe mutum 222, an yi wa 20 fyade a wata 3 a Kaduna – Rahoto
Amma jami’an tsaro sun yi namijin kokari wajen yin dauki-ba-dadi da su kafin daga bisani su cimma su.
A wasan karshe na gasar Ingila ta yi rashin nasara a hannun Italiya a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-raga.
Ingila ta shafe shekara 55 kafin samun nasarar zuwa wasan karshe na kowace gasa a kwallon kafa a duniya.