✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EU ta gargadi China kan taimaka wa Rasha

EU ta gargadi China a kan taimakon shugaba Putin a yakinsa da Ukraine.

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta gargadi China a kan taimaka wa Rasha makamai a yakin da ta ke yi da Ukraine.

EU ta kuma bukaci China a kan kada ta kuskura ta taimaka wa shugaban Rashar Vladmir Putin dangane da takunkuman da kasashen Yammacin Duniya suka kakaba masa.

Shugaba Xi Jinping na China wanda har yanzu ya ki fitowa fili ya yi Allah wadai da matakin da Rasha ta dauka na mamayar Ukraine, zai yi wata tattaunawa ta bidiyo da jami’an tarayyar turai ciki har da shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar, Ursula von der Leyen.

Za a yi taron ne ta bidiyo a lokacin da alaka tsakanin Tarayyar Turai da China ta yi tsami.

A farkon watan Fabrairu, China da Rasha suka fitar da wata sanarwa wadda a ciki suka bayyana cewa alakarsu na nan daram.

Shugabannin tarayyar turai sun damu kan abin da suka gani a matsayin wata manufa ta sake fasalin tsari da manufar duniya, daga wannan sanarwa da kasashen biyu suka fitar kan alakarsu.

Jami’an tarayyar turai a yanzu sun yi amanna gwamnatin Rasha ta bukaci taimakon soji daga China da kuma taimakon da za ta samu sassauci daga takunkumin da aka sanya mata.

Kafofin yada labarai na tarayyar turai sun ce shugaba von der Leyen za ta bukaci shugaba Xi na China da ya yi watsi da bukatun da Rasha za ta bijiro masa, a maimakon haka shugaban ya yi amfani da karfin China wajen kawo karshen yakin da ke wakana.

Sai dai ministan harkokin wajen China a wannan makon ya yaba wa Rasha ne inda ya ke cewa alakarsu da Rasha na tafiya yadda ya kamata.

Jami’an tarayyar turai ba sa tsammanin samun wata yarjejeniya ta a zo a gani a taron da za su yi a ranar Juma’a, amma dai suna sa ran shawo kan China ta sa shugaba Putin da kada ya yi amfani da makaman kare dangi a yakin da yake yi da Ukraine.