Golan Najeriya bincent Enyeama da ke buga kwallo a kulob din Lille na Faransa ya bayyana cewa ba zai samu damar halartar wasan share fage na zuwa gasar cin kofin Afirka a tsakanin Najeriya Super Eagles da Kongo a garin Kalaba a gobe Asabar ba saboda matsalolin da suka shafi iyali.
Golan, yana daga cikin gololi uku da Koci Stephen Keshi ya gayyato don yin wasan da suka hada da Austin Ejide da kuma Chigozie Agbin da ke kama wa kulob din Gombe United kwallo.
“Na kira koci Stephen Keshi na shaida masa halin da nake ciki da kuma dalilin da ya sa ba zan samu halartar wasan ba amma na ba shi tabbacin nan gaba idan ya sake gayyata zan halarta amma dai a wannan karo ba zan samu dama ba”, inji Enyeama.
Najeriya za ta yi wasan farko ne da Kongo a gobe a Kalaba kafin ta yi wasanta na biyu da kasar Afirka ta Kudu a birnin Cape Town.
Enyeama ba zai yi wasan Kongo da Najeriya ba
Golan Najeriya bincent Enyeama da ke buga kwallo a kulob din Lille na Faransa ya bayyana cewa ba zai samu damar halartar wasan share fage…
