Majalisar Wakilai ta ce za ta ware kudade a kasafin 2021 domin biyan diyya ga mutanen da tsautsayi ya ritsa da su a zanga-zangar kyamar sashen ’yan sanda na FSARS.
Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ya fadi haka ne a ranar Talata inda Majalisar ta yi shirun minti daya domin juyayin wadanda suka mutu a lokacin zanga-zangar.
- Majalisa ta fara aiki kan kasafin 2021
- Atiku ya nemi Buhari ya janye kasafin kudin 2021 da ya gabatar
Ya ce “A makon jiya Majalisar Wakilai ta cimma matsayi a kan batun wanda hakan ke nuna mahangarmu daya da na ‘yan Najeriya.
“A kawo mana jerin sunayen wadanda suka mutu domin mu ware musu kudaden da za a biya iyalensu daiyya daga kasafin kudi”, inji shi.
Gbajabiamila ya ce ware kudaden na daga cikin matakan da Majalisar Wakilai ta dauka na tabbatar da kare rayukan ‘yan Najeriya da kuma biyan diyya ga iyalan wadanda da aka kashe a wuraren zanga-zangar a sassan Najeriya.
‘Za a biya masu zanga-zanga diyyar miliyan N200’
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan Jihar Legas ya yi alkawarin kaddamar da gidauniyar Naira miliyan 200 domin biyan diyya ga wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar a Jihar.
Gwamnan Babajide Sanwo-Olu ya sanar da haka a lokacin da yake jawabi ga taron masu zanga-zangar a Majalisar Dokokin Jihar.
Sanwo-Olu ya ba da umarnin a saki masu zanga-zangar da ake tsare da su nan take.
Gwamnan ya bukaci a mika wa gwamnain jihar sunayen wadana aka kashe tare da ba wa taron tabbacin kwato hakkin wadanda aka zalunta a lokacin zanga-zangar.
Ya yi musu alkawarin gabatar da koken masu zanga-zangar wadanda suka bukaci a yi wa ‘yan sanda karin albashi sannan a hukunta wadanda ke da hannu wurin gallaza wa masu zanga-zangar.