✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: ’Yan sanda sun ba ‘barayin’ makamai wa’adin kwana 7

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Edo ta ba da wa’adin kwanaki bakwai ga matasan da suka farfasa dakunan ajiyan kayan gwamnati suka saci kayan abinci…

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Edo ta ba da waadin kwanaki bakwai ga matasan da suka farfasa dakunan ajiyan kayan gwamnati suka saci kayan abinci da makamai a ofisoshinyan sanda a yayin zanga-zangar #EndSARS su dawo da su ko su fuskanci hukunci.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Johnson Babatunde Kokumo ya yi gargadin a birnin Benin yayin da yake bayani kan makaman da masu zanga-zangar suka sace.

“Daukar makamai na daga cikin alamomin ta’addanci, don haka muna kira da wadanda suka dauki kayan cewa lallai su dawo da su cikin kwanaki bakwai daga ranar Litinin 9 ga Nuwamba.

Kwamishin ya ce, bayar da wa’adin ya zama tilas sakamakon harin da masu zanga-zangar #EndSARS suka kai wuraren gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a fadin jihar.

“Rashin bin wannan gargardi zai sanya rundunar ’yan sanda daukar matakin doka da kama duk wanda aka samu yana da hannu a ciki”, inji shi.

Kokumo, ya yi alkawarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar da kuma bayar da tukuici ga duk mutumin da ya bankada asirin wadanda suka aikata laifin ta kai ga kama barayin makaman.

Ya nemi hadin kan jama’ar yankin da lamarin ya faru su bayar da gudunmawa ta hanyar bayanai domin ’yan sanda ba za su iya gudanar da aikin su kadai ba.