A yayin da zanga-zangar kin jinin rundunar SARS ke ci gaba da daukan sabon salo, ’yan daba sun kai hari a wani gidan kaso a birnin Benin inda suka kubutar da fursunoni da dama.
’Yan daban sun kuma lalata ginin wata Babbar Kotu da ke makwabtaka da gidan yarin.
- An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Edo
- Arewa ake neman karyawa da zanga-zangar #EndSARS —Sheikh Jingir
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne yayin da ’yan daban suka yi dandazo tun da misalin karfe 7.00 na safiyar Litinin tare da kunna wata a kan tituna.
Ganin yadda lamarin ke neman wuce gona da iri, Gwamnatin Jihar Edo ta shimfida dokar ta-baci ta tsawon awa 24, sakamakon harin da aka kai wa ’yan sanda da kuma kubutar da fursunoni daga gidan yarin da ke Benin, babban birnin Jihar
A sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Edo Osarodion Ogie ya fitar, ta ce dokar hana fitar “za ta ci gaba da kasancewa har sai baba ta gani.”
Ogie ya ce ’yan daba sun kwace iko da zanga-zangar #EndSARS kuma “ba zai yiwu gwamnati za ta zura ido ba yayin da ake kai hare-hare.”
Yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin gidajen yari na jihar, ASP Aminu, ya ce zai bayar da sanarwa nan ba da jima wa ba.