✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: SERAP ta maka Gwamnatin Buhari a Kotun Duniya

Kungiyar SERAP mai sa ido kan ayyukan Gwamnati ta yi karar Gwamnatin Buhari a Kotun Duniya

Kungiyar SERAP mai sanya ido kan ayyukan Gwamnatin Najeriya ta kai karar Gwamnatin Buhari gaban Kotun Duniya.

SERAP ta bukaci kotun duniya ta yi bincike kan ’yan siyasa, jami’an tsaro da sauran wadanda ake zargi da hannu wajen daukar ’yan daba da suka kai hare-hare kan masu zanga-zangar #EndSARS a sassan kasar.

Ta roki kotun ta yi bincike a tsanake ta gano da kuma hukunta masu daukar nauyin tada hankulan jama’a domin zama izina ga wasu a nan gaba.

Kungiyar ta bukaci shugabar kotun Fatou Bensouda ta hukunta duk wanda aka kama da hannu a cikin tashin-tashinar da ta auku.

Ta shigar da karar ne bayan kasha-kashe da bata dukiyoyi da wasu bata-gari suka yi musamman a jihohin Legas, Abuja, Kano, Edo, Filato, Abia da Anambra.

Lamarin ya fi kamari a Jihar Legas, in gwamnatin jihar ta sanya dokar hana walwala domin dakile ayyukan bata-garin.

A ranar Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba wa masu zanga-zangar ta #EndSARS hakuri da kuma tabbacin gwamnatinsa za ta kawo gyara a hukumar ’yan sanda baki daya.