Ministan Labarai da Al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya sake yin fatali da rahoton da ke tabbatar da zargin kisan ’yan Najeriya a zangar-zangar #EndSARS da aka yi a bakin kofar shiga unguwar Lekki da ke Jihar Legas.
A wani taron manema labarai da ya gudana ranar Talata a Abuja, Lai Mohammed ya ce rahoton da kwamitin bincike da gwamnatin Jihar Legas ta kafa ya gabatar ba wani abu ba ne face shaci-fadi da kanzon kurege.
- WAEC ta kara kudin jarrabawa daga N13,950 zuwa N18,000
- Abin da sakin Nnamdi Kanu zai haifar a Najeriya — CNG ta gargadi Buhari
A makonnin da suka gabata ne wani Kwamiti daga bangaren shari’a da gwamnatin Jihar Legas ta kafa ya gabatar da sakamakon binciken wanda ya tabbatar da zargin harbe-harben da sojoji da ’yan sanda suka yi kan ’yan Najeriya yayin zanga-zangar #EndSARS da ta gudana a bakin unguwar Lekki a bara.
Sai dai yayin da yake mayar da martani, Ministan Labarai da Al’adu ya ce wannan rahoto da aka gabatar ya sake jadadda yadda ake yada labaran karye a kafofin sadarwa na intanet tun daga lokacin faruwar lamarin a watan Oktoban bara har zuwa yanzu.
Lai Mohammed ya ce, “a tarihi ba a taba samun wani kwamiti na shari’a ba da ya gabatar da rahoto kan wani bincike mai cike da kura-kurai, shaci-fadi da rashin sahihan bayanai wadanda ba su da madogara da kwararan dalilai ko hujjoji.
“Abin da yake yaduwa a yanzu wani maimaici ne na kanzon kurege da labaran karya da suka rika yaduwa a kafofin sadarwa na intanet tun daga ranar 20 ga watan Oktoban 2020 har ya zuwa yanzu.
“Abin mamaki a ce irin wannan kwamiti na shari’a da aka kafa domin bincike a kan lamarin ya gabatar da rahoto mai cike da bayanai na zargi da rashin tabbas.
“A maimakon shafe shekara guda da aka yi wajen gudanar da bincike a kan lamari, da kawai wannan kwamiti shi ma ya bi ’yan yarima a sha kida wajen gabatar da tatsuniyoyin da aka rika yadawa ba tare da asarar kudin gwamnati ba da bata lokaci kowa ba.
A cewar Lai Mohammed, zargin kisa ba karamin abu ne wanda ba zai dogara kadai ba a kan zargi ba, inda ya bayyana cewa an fitar da rahoton ne kadai domin a kunyata gwamnati da hukumominta ba tare da hujjoji ba.
Ya ce babu yadda za a yi gwamnati ta bari hukumominta na tsaro su ci zarafi ko keta hakkin ’yan Najeriya ba ta kowace irin hanya, ya ce dalilin da ya sa aka soke Rundunar ’yan sanda ta SARS tare da karfafawa jihohi su kafa kwamitin bincike kan rahotannin take hakkin dan Adam da ake zargin ’yan sanda na SARS na yi.